Mali na ci gaba da neman dunke baraka
July 29, 2020Talla
Firaministan na kasar Mali Boubou Cisse, ya bukaci Imam Mahmoud Dicko, wanda a hannu guda babban malami ne mai wa'azin addinin Islama da kuma ke da karfin fadi a ji, da ya karbi tayin sasanci da gwamnati ta bayar, musamman ma wajen shawo kan jiga-jigan masu zafin adawa da gwamnatin.
A ranar Litinin da ta gabata, kungiyar ECOWAS ta bukaci Shugaba Ibarhim Boubacar Keita da ya samar da gwamnatin hadaka, sannan ya yi gyara ga kura-kuran siyasa ta suka haddasa husumar da kasar ta fada.
Sai dai a nasu bangaren masu adawa da gwamnatin na Mali, sun yi watsi ne da shawarar ta ECOWAS, wadda wasu shugabannin Afirka ta Yamma suka bayar a zama karo na biyu da suka yi a Bamako abban birnin kasar.