Mali na neman 'yan kasashen ketare da aka sace ruwa-a-jallo
September 25, 2025
Talla
Gwamnatin Mali ta sanar da sace wasu 'yan asalin Hadaddiyar Daular Larabawa biyu da wani dan Iran guda a makon da ya gabata a kusa da Bamako babban birnin kasar.
Ficewar kasashen AES daga kotun ICC
A cikin wata sanarwar da ma'aikatar tsaron cikin gidan Mali ta fitar a ranar Alhamis, gwamnatin ta ce an sace mutanen ne a makon jiya, kuma tana iya kokarinta domin ganin ta kubutar da su.
Kungiyar Kasashen yanki Sahel ta cika shekaru
Tun a shekarar 2012 kasar Mali da yanzu haka ke karkashin mulkin soja ke fama da mummunar matsalar tsaro, wacce ta samo asali daga tashe-tashen hankula na kungiyoyi masu tayar da kayar baya masu alaka da Al-Qaïda da IS, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama ciki har da mata da kananan yara.