1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ta'addanciAfirka

Mali na rubanya farmaki kan 'yan ta'adda domin murkushe su

June 10, 2025

Sojojin Mali sun kaddamar da farmakin ramuwar gayya bayan hare-haren da 'yan jihadi suka kai a sassan kasar. Babban hafsan sojin kasar ya ce hare-haren da suka kai sun haddasa mummunar asara tsakanin 'yan ta'adda.

Janar Assimi Goita ya sha alwashin ganin bayan ayyukan ta'addanci a Mali
Janar Assimi Goita ya sha alwashin ganin bayan ayyukan ta'addanci a MaliHoto: AP Photo/picture alliance

A cewar babban hafsan sojin kasar Mali, Janar Oumar Diarra, an gano sansanoni da dama da ake amfani da su wajen shirya hare-haren ta'addanci a tsakiya da arewacin Mali.  A yayin farmakin da rundunar dakarun FAMA ta kaddamar, wanda ya hada da sojojin kasa da na sama, sojojin Mali sun yi wa 'yan ta'adda rubdugu daga ko'ina. Hatta mazauna birnin Bamako sun shaida cewa jiragen yaki sun rika kai da kawo a lokacin fadan a sararrin samaniyar Bamako.

Djibril,  wani mazaunin birnin Bamako ya ce: "jiragen marasa matuka na ta yin shawagi kasa-kasa, ba manyan jiragen yaki ba ne . Da su ne ke shawagi a kan dakunanmu da an yi barna. Kuna na iya bambanta tsakanin hayaniyar jiragen sama da jirage marasa matuka. Jirgin mara matukin ya yi kasa-kasa a kusa da unguwanni kamar Faladiè ko Niamakoro, da ke cikin Bamako, mun shaida."

Karin bayani:AES: Tsayawa da kafa ko kara shiga matsala?

Jiragen sama na taka muhimmiyar rawa a fannin yaki da ta'addanci a kasar MaliHoto: Speich Frédéric/Maxppp/dpa/picture alliance

Tun da farko, sojojin kasar Mali sun fice daga daya daga cikin manyan sansanonin sojin kasar da ke yankin tsakiyar kasa., bayan hare-hare biyu da masu ikirarin jihadi suka kai a sansanin, inda sojoji da dama suka rasa rayukansu. Harin da aka kai a sansanin Boulkessi da ke a tsakiyar Mali ya janyo asarar rayukan sojoji da dama, a cewar wani jami'in yankin,  wanda ya bayyana cewa sojojin Mali na karshe da ke cikin sansanin sun arce daga cikinsa. Hakan ya janyo fusatar dakarun FAMA da suka mayar da martani karfaffa.

Ga abinda wannan mutumin mai sunan Ahmed yake cewa: "Idan wadannan jiragen da muke jin karar shawaginsu ba dare ba rana suna aikin latata cibobiyin yan ta‘adda ne, hakan wani  abu ne mai kyau. Amma shin da gaske haka lamarin yake? Domin a matsayinmu na mutane daga tsakiyar kasar, mun lura cewa jiragen sojojinmu kan zagaya ba tare da tarwatsa masu jihadi ba.".

Karin bayani:Juyin mulki bai hana rashin tsaron Sahel ba

Sojojin rundunar FAMA na aiki ba dare ba rana domin kawar da hare-haren ta'addanciHoto: Philippe De Poulpiquet/MAXPPP/dpa/picture alliance

Hare-haren sojojin Mali na mayar da martani  sun zo ne a daidai lokacin sanarwar da rundunar dakarun Wagner na Rasha ta yi, na kawo karshen ayyukanta a Mali. Yanzu haka dai, rundunar sojojin Afirka ce ta maye gurbinta, wacce ta fara aiki a karkashin kulawar ma'aikatar tsaron kasar Rasha. A hukumance dai, gwamnatin Mali ta amince da kasancewar sojojin Wagner na  Rasha tun daga 21 ga watan Disamba na shekara ta 2021. 

Mali na fama da tashe-tashen hankula daga kungiyoyin masu ikirarin jihadi da ke da alaka da Al-Qaeda da IS. Tun a shekara ta 2012, birnin Timbuktu ya kasance karkashin ikon mayakan jihadi na tsawon watanni.