1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Halitta da MuhalliMali

Samar da abinci da kare muhalli a Mali

October 23, 2025

A wani mataki na kawo sauyi da inganta muhalli da kuma samar da kudin shiga, wani matashi a kasar Mali ya soma sarrafa 'yayan bishiyar kuka wajen yin abun sha da kuma samar da tsirrai da za a shuka nan gaba.

 Mali | Kare Muhalli | Samar da Abinci | Bunkasa Tattalin Aziki
Matashin da ke alkinta itacen kuka da kare muhalli da kuma samar da abinci a MaliHoto: DW

Matashin kuma Injiniyan aikin gona Ichaka Dambele ya kafa kamfaninsa a Bamako babban birnin kasar Mali, inda yake samar da hodar kwame daga 'yayan itatuwan Kuka. Matashin ya sha alwashin taimakawa al'umma da kuma kare itacen da ake sarewa, a wani gandun dajin kasar. Ichaka Dambele ya ce: "Dajin yana da fa'ida ta fuskar tattalin arziki, saboda haka muka saka wa kamfanin suna Forêt Forte Mali''.

Illolin sare dazuzzuka

Yawancin dazukan kasar Mali suna fuskantar lalacewa, inda a kowace shekara kusan hekta 100 ke lalacewa. Wannan yanki da ake samun bishiyar kuka wasu masu kona gawayi ne ke ziyarar yankin a baya amma a yanzu wannan matashi ya soma aiki da wata kungiyar mata da suke aiki tare, inda suke taimaka masa da aiki sarrafa 'yayan itatuwan kukar wajen ganin garin hodar ya kasance mai tsafta.

Ambaliya ta haddasa barna a Mali

01:57

This browser does not support the video element.

Matashi Dambele ya dukufa wajen ganin hakarsa ta cimma ruwa a kan ingata muhalli, baya ga samar da kudin shiga kamar yadda yake cewa: ''.......mun samar da wani dandali mai suna "G4 Environment", wanda ya dasa bishiyoyi sama da dubu 10 a bara tare da kungiyoyi sama da 30. Mun samu gagarumar nasara, kuma sama da matasa 1,000 sun shiga cikin shirin."

Samar da abinci kare muhalli da samun kudin shiga

Wannan garin hodar 'yayan bishiyar kukar da matashin da wasu ma'aikatansa ke samarwa, yana kunshe ne da sinadiran Vitamin C da kuma Calcium. A yanzu dai matasan sun dukufa wajen samar da tsirran bishiyar kuka kuma ana aikin shuka ta a kamfaninsa, inda matasan da ke aiki karkashinsa ke taimaka masa wajen sake dasa itacen domin samar da bishiyoyi masu kyau da inganci nan gaba a kasar Mali.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani
Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW