Yankin Gao na Mali ya cika shekaru 10 da tashin hankali
March 31, 2022Yankin Gao da ke arewacin Mali na zama wani tushe na tashe-tashen hankula da aiyukan ta'addanci da ke addabar arewacin Mali da ma wasu kasashen yankin Sahel.
Shekaru uku bayan da ta ayyana daular Islama, kungiyar MUJAO mai ikirarin jihadi ta fara zartar da hukunci irin na shari'ar Musulunci. Wannan ya sa da dama daga cikin al'umma a yankin na Gao musamman ma mata suka guje wa birnin domin samun mafaka a wasu manyan biranen da ke kusa da garin. Burinsu shi ne kauce wa ayyukan cin zarafin bil'Adama da na kisan gilla da suke zargin sababbin masu iko da yankin ka iya aikata musu.
A ranar biyar ga watan Afrilun 2012, Mariam Diawara, da ke zaune a yankin ta yi hijira daga Gao bayan da mayakan jihadi suka karbe iko daga hannun kungiyar MNLA. Diawara ta kaura don tsira da ranta, in da ta koma birnin Bamako. Ta ce tana tune da irin abubuwan da suka wakana a wancan lokacin a mahaifarta ta Gao wadanda ta kira na bakin tarihi.
''Lokacin da yaki ya barke an tilasta mana barin Gao, domin ana yin garkuwa da mata da yara. Ana rusa gidaje tare da kare dukiyoyin al'umma. Ana kashe maza kama daga fararen hula har zuwa soja kuma hakan bai bar hatta ma wani ma'aikacin gwamnati ba'' inji Mariam
Da haka ne dai yankin na Gao ya shafe tsawon shekaru 10 a hannun kungiyoyin 'yan bindiga masu ikrarin jihadi dabam-dabam. Kazalika haka shi ma daya birnin mai cikakken tarihi na waliyai, Tombouctou, ya kasance karkashin ikon kungiyoyin, in da suka rusa muhimman wuraren tarihi tare da kafa dokokinsu na shari'ar Maulunci.
Sai dai a shekarar 2013, tare da taimakon sojan Faransa na ''Seval'' gwamnatin Mali ta sake karbe iko a hannun 'yan bindigar. To amma kuma kawo yanzu yankin na arewacin Mali da kusan kudanci har ma da kasashe makwabtan Mali na dandana kudarsu da hare-haren 'yan ta'adda.