1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceMali

Mali: Shekaru biyar bayan juyin mulki

Suleiman Babayo
August 18, 2025

Shugaban gwamnatin mulkin sojan Mali Assimi Goita na kara kankame madafun iko yayin da lamura ke kara sukurkucewa a kasar

Faretin sojojin Mali
Faretin sojojin MaliHoto: Florent Vergnes/AFP/Getty Images

Lamura tsaro sun tabarbare a kasar Mali, Jama'a na zaman zulumi bayan zargin ministan tsaron kasar Janar Daoud Aly Mohammedine da yunkurin kifar da gwamnati a makon da ya gabata, tare da zargin ya samu taimako daga kasashen ketere. Gwamnatin mulkin sojan ta Mali ta zargi wani dan-Faransa da hannu gami da wasu jiga-jigan sojojin kasar. An shiga yanayin rashin tabbas saboda masu mulkin kasar suna nuna rashin yarda da kowa.

Paul Melly na cibiyar kula da harkokin kasashen ketere na Chatham House da ke birnin London na Birtaniya yana ganin matsalolin sun wuce yadda ake tunani na mayar da kasar bisa tafarkin dimukuradiyya:

Karin Bayani: Mali ta cafke wani Bafaranshe kan zargin yi wa hukumar leken asirin Faransa aiki

"Mali yanzu haka tana fuskantar kalubale daga bangarori da dama fiye da batun shirin mayar da kasar bisa tafarkin dimukuradiyya, kuma yaushe za a koma daga tsarin sojoji zuwa tsari na gwamnatin da jama'a suka zaba."

Hoto: AFP

Masanin ya kara da cewa yanayin da ake ciki na da tsauri saboda yadda kungiyoyin Jihadi ke ci gaba da kai hare-hare a kasar da ke yankin yammacin Afirka har da kasashe makwabta na Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar.

Wannan yunkurin juyin mulki na Mali na zuwa shekaru biyar bayan juyin mulkiin da ya kifar da gwamnatin farar hula ta Ibrahim Boubakar Keita a shekara ta 2020. Sannan sojoji suka sake wani juyin mulkin a shekara ta 2021. A lokacin Janar Assimi Goita ya mayar da kasar karkashin mulkin sojoji. Daga bisani kasashe makwabta na yankin Sahel na Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar suka bi sahun Mali inda sojoji suka kwace madafun iko. Kasashen sun fice daga cikin kungiyar ECOWAS tare da kirkirar kungiyar AES. Sannan suka katse hulda da kasashen Yamma suka koma bangaren Rasha.

Karin Bayani:Hukumomin kasar Mali sun kama akalla sojoji kusan 20

Ulf Laessing na Gidauniyar Konrad Adenauer da ke kasar ta Mali ya yi tsokaci.

Hoto: AP Photo/picture alliance

"A gaskiya manufofin gwamnatin mulkin sojan sun banbanta da na kasashen Yammacin Duniya, inda suka myar da hankali wajen samun taimako daga Rasha kuma akwai banbance-banbance cikin sojojin kasar. Ana ci gaba da cin zarafin mutane yayin da tsageru ke kai hare-hare na kashe fararen hula, sannan lamuran tsaro suka sukurkuce. An yanke tsammanin cewa Rasha da ke da sojojin haya kamanin 1,500 za ta taimaka wajen kawo zaman lafiya."

Karin Bayani:Assimi Goita ya rusa kungiyoyi da jam'iyyun Siyasar kasar Mali

Zai yi matukar wuya da kalilan na sojojin haya na Rasha a shawo kan matsalolin tsaron da kasar Mali ke ciki, yanzu kuma shekaru biyar ke nan tun bayan juyin mulkin bisa alkawarin fitar da kasar daga cikin matsalolin tsaro.