1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS za ta yi sabon taro kan Mali

September 14, 2020

Shugaban kasar Ghana kana shugaban karba-karba na kungiyar ECOWAS ko CEDEAO, Nana Akufo-Addo ya kira taron tuntubar juna a kusa da birnin Accra, domin neman hanyar warware rikicin siyasar Mali.

Mali I Treffen von Deligierten in Bamako
Taron masu ruwa da tsaki kan kafa gwamnatin rikon kwarya a MaliHoto: picture-alliance/AP

Wannan mataki ya zo ne kwanaki biyu bayan matsayar da babban taron kasar Malin ya cimma na kafa gwamnatin rikon kwarya ta tsawon watanni 18, matakin kafa gwamnatin rikon kwaryar kuma da kungiyar gwagwarmaya ta M5 ta yi fatali da shi. Kwamitin mulkin sojan Malin na CNSP ne dai ke da alhakin nada wadanda za su jagoranci rikon kwaryar, imma farar hula ne ko soja. Dama dai babban taron kwanaki uku da sojojin suka shirya a birnin Bamako, ya tanadi mukamin shugaban rikon kwarya da mataimakin shugaban rikon kwaryar da kuma majalisar rikon kwarya ta kasa da za ta kunshi mambobi 121 ta gwamnatin mai mambobi 25.

Karin Bayani:  Mali: Kalubalen gwamnatin mulkin soja

Tuni dai tsohon Firaministan kasar ta Mali Moussa Mara ya nuna kyakkyawan fata dangane da alkiblar da aka dosa wajen fitar da kasar daga mawuyacin halin da ta samu kanta a ciki: "Burinmu shi ne hada kan 'yan Mali gaba daya, sannan kuma mu iya farfado da hulda da kasashen duniya. Don haka mun amince da aikin CNSP da sauran shugabannin da ke aiki tukuru, domin aikinmu na hadin gwiwar da ECOWAS ko CEDEAO ya gudana cikin yanayi mai kyau."

Firaministan Mali Moussa MaraHoto: Privat

Kwamitin mulkin sojin na Mali zai gana da shugabannin ECOWAS a wannan Talata, kwaniki kalilan bayan da suka dage kai da fata cewar wa'adin shekara guda kadai suka baiwa gwamnatin rikon kwaryar da ake shirin kafawa. Yayin da bangarorin da suka shiga tattaunawar kasa suka amince da rikon kwarya na tsawon watanni 18 domin a karfafa tsaro a duk fadin kasar, tare da daura damarar shirya babban zabe a kasar. Dramane Yalcouye ne shugaban matasa na Ginna Dogon, wato kungiyar da ke karewa tare da habaka al'adun Dogon, ya ce bai ga abin kushewa a wannan tsari ba. "Zai iya ma'ana idan hukumomin rikon kwarya na watanni 18 suka iya nasarar aza tubalin kafa sabuwar Mali."

Karin Bayani: Jerin takunkumi bayan juyin mulki a Mali

Sai dai ana fuskantar rashin tabbas game da wanda ya kamata ya zama sabon shugaban rikon kwaryar kasar ta Mali, a cewar Coumba Bah kwararre a fannin sadarwa. "Har yanzu akwai sauran aiki a gaba a kan yadda za a samu matsaya kan wannan sabon shugaban rikon kwarya da mataimakin shugaban kasa ko mataimakiyar shugaban rikon kwarya, da ma wannan gwamnatin da za ta kunshi mambobi 25 ko kasa da haka da za a kafa."

Jagoran gangamin kifar da gwamnatin IBK a Mali, Imam Mahmoud DickoHoto: Reuters/R. Byhre

Amma kuma ra'ayin gamayyar kungiyar 'yan adawa da 'yan farar hula ta M5, ya sha bamban a kan matsayar da aka cimma a Mali. Cikin sanarwar da ta fitar a birnin Bamako, ta fito fili ta yi watsi da shirin, tare da zargin sojoji da nuna son rai. Sannan kuma ta kara da cewa  daftarin da aka samar ba shi da wata ma'ana saboda ya saba da abin da 'yan Mali ke so.

Karin Bayani: Sharhi kan matsalolin da ke tunkarar Mali

Choguel Kokalla Maiga da ke shugabantar kungiyar ta M5, ya yi tir da abin da ya kira yunkurin sojoji na kakkange madafun iko: "M5-RFP ta yi Allah wadai da rashin la'akari da bangarori da yawa na batutuwa da aka amincewa, ba tare da samun amincewar kowa ba. Wadannan batutuwa sun hada da tarurrukan kasa domin sake dora ta a kan kyakkawan tsari da hukumar kula da tsarin rikon kwarya da kwamitin ba da shawarwari. Saboda haka kungiyar M5-RFP ta yi tir da tursasawa, da dabi'un da ba su dace da dimukaradiyya ba, wadanda aka yi amfani da su a wani zamani na baya, wanda gwagwarmayar kawo canji ta yi awon gaba da su."

Shugabannin kasashen ECOWAS ko CEDEAO za su tattauna tsakaninsu, domin amincewa ko watsi da sabon tsarin tafiyar da kasra ta Mali.  A ranar 18 ga watan Agusta ne dai, sojoji suka yi wa tsohon shugaba Ibrahim Boubacar Keita juyin mulki, wanda shi ne irinsa na hudu a kasar tun bayan samun 'yancin kanta daga Turawan mulkin mallaka na Faransa a shekarar 1960.