Gwamnatin Mali ta bayyana shirin matakan tsaro a Ogossagou
March 25, 2019Talla
Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya kai ziyarar gani da ido a yau Litinin a kauyen Ogossagou da ke yankin tsakiyar kasar inda aka yi wa fulani fararen hula kisan kiyashi a karshen makon jiya. Akalla Fulani 130 ne suka mutu galibi mata da yara sakamakon wani harin da mayakan sa kai 'yan kabilar Dogons suka kai a garin na kabilar Fulani zalla.