1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a kafa gwamnatin rikon kwarya a Mali

Abdul-raheem Hassan
September 13, 2020

Shugabannin sojojin da ke mulki a Mali bayan kifar da gwamnatin Ibrahim Boubakar Keita, sun amince da kafa gwamnatin rikon kwarya ta watanni 18 da zai kai ga shirya sabon zabe.

Mali I Colonel Assimi Goita
Hoto: Reuters/M. Rosier

An cimma wannan yarjejeniyar bayan tattaunawar kwanaki uku tskanin kungiyoyin fararen hula da 'yan adawa a Bamako babban birnin kasar Mali.

Kakakin shugaban juyin mulkin na Mali Mousa Kamara, ya ce sojoji za su nada kwamitin zaben shugaban gwamnatin rikon kwarya da mataimakin da za su jagoranci kasar tsawon watanni 18.

A baya sojojin da suka yi wa Ibrahim Boubakar Keita juyin mulki, sun bukaci mulkin kasar na tsawon shekaru biyu, amma matakin ya fuskanci matsin lamba daga kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS da sauran kasashen duniya.