1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali ta ce ba za ta tattauna da kungiyoyin 'ta'adda' ba

May 8, 2026

Gwamnatin Mali ta ce ba za ta tattauna da kungiyoyin masu dauke da makamai ba bayan sabbin hare-hare da suka afka wa wasu garuruwa. Hare-haren dai sun kara dagula matsalar tsaro a kasar.

Shugaban kasar Mali Kanal Assimi Goita
Shugaban kasar Mali Kanal Assimi GoitaHoto: OUSMANE MAKAVELI/AFP/Getty Images

Gwamnatin mulkin soja a Mali, ta ce ba za ta tattauna da kungiyoyin masu dauke da makamai da take kira ‘yan ta'adda ba, bayan hare-haren da mayakan jihadi da masu neman ballewa suka kai wa gwamnatin mulkin soja.

Hare-haren da aka kai a ranakun 25 da 26 ga watan jiya, sun afka wa muhimman garuruwa tare da kashe ministan tsaron kasar.

Ministan harkokin wajen Mali Abdoulaye Diop ya ce gwamnati ba ta da niyyar yin tattaunawa da kungiyoyin da ke dauke da makamai, yana mai cewa suna da alhakin rikicin da kasar ke fama da shi tsawon shekaru.

Ya ce Mali ta sha fama da rikicin tsaro sama da shekaru goma, kuma wadannan hare-hare sun tuno da rikicin da ya barke a 2012.

Sabuwar kawance tsakanin kungiyar Azawad Liberation Front da kungiyar JNIM mai alaka da al-Qaeda ce ta kai sabbin hare-haren.