Mali ta dakatar da ayyukan yakar ta'addanci da Faransa
September 26, 2025
Wadannan bayanan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ma'ikatar harkokin kasashen ketare ta Mali ta fidda a tsakiyar wannan watan sai dai ba su bayyana dalilan koran jami'an diplomasiyyar ba.
Wani jami'in diplomasiyyar Faransa ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewar matakin na da nasaba da wanda Faransa ta dauka na korar wasu jami'an Bamako biyu daga birnin Paris.
Takaddamar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu na karuwa a 'yan kwanakin baya-bayan nan, bayan kama wani jami'in leken asirin Faransa a watan Augusta da mahukuntan Mali suka yi.
Hukumomin Mali sun zargi kasar Faransa da yunkurin shirya juyin mulki tare da taimakon wasu sojojin kasar ciki har da manyan hafsoshin soji biyu da tuni aka kama su.
Karin Bayani: Mali ta amince Goita ya ci gaba da mulki har 2030