1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An dakile harin 'yan ta'adda a Mali

Abdoulaye Mamane Amadou Abdul-raheem Hassan
September 3, 2023

Rundunar tsaro a kasar Mali ta yi ikirarin murkushe wani harin ta'addancin da wasu mahara suka kai a wani shingen bincike da ke wajen Bamako babban birnin kasar.

Hoto: Fatoma Coulibaly/REUTERS

Ma'aikatar tsaron kasar Mali ta ce jami'an 'yan sandan da ke gadi a wani shingen bincike na Dialakoroba sun mayar da martani, bayan wasu mahara sun bude wuta kan jami'an da ke gadi a wurin binciken, har ma sun kashe wani dan ta'adda daya.

Hukumomin kasar Mali sun ruwaito cewar bata-kashin ya raunata wasu 'yan sanda uku da fararen hula biyu. Tun a shekarar 2012 kasar Mali ke fuskantar hare-haren masu ikrarin jihadi, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Bayan kifar da gwamnatin farar hula ta  Ibrahim Boubacar Keita a shekarar 2020, sojojin da suka jagoranci juyin mulkin sun yanke kauna da kasar Faransa da ta yi wa Mali mulkin mallaka tare da karkata alakarsu ta siyasa da ta fannin tsaro ga kasar Rasha.