Tattalin arzikiAfirka
Mali ta karya watsi da kudin Cefa
January 27, 2026
Talla
Kasar Mali ta musanta rahotannin da ke cewa kasar da sauran biyu na Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar na kawancen Sahel suna shirin watsi da takardar kudin Cefa da kasashe rainon Faransa na Yammacin Afirka suke amfani da shi.
Dalilin watsi da jita-jitar
Hukumomin mulkin sojan kasar ta Mali sun ce babu kamshin gaskiya game da rahoton, kuma ba yi da tushe bare makama na cewa gwamnatocin mulkin sojan kasashen uku za su fitar da sabon kudin da za su koma amfani da shi. Ma'aikatar kudin kasar ta Mali ta karyata batun ficewar.
Kasashen uku na Mali da Burekina Faso gami da Jamhuriyar Nijar sun fice daga cikin kungiyar ECOWAS inda suka koma kawance Sahel bayan sojoji sun karbe madafun ikon kasashen uku na yammacin Afirka.