1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An saki sojojin Ivory Coast

Ramatu Garba Baba
January 7, 2023

Gwamnatin Mali ta bayar da umarnin sakin sojojin kasar Ivory Coast kimanin 49 da take tsare da su a bisa zargin yi wa tsaron kasar zagon kasa.

Hoto: ISSOUF SANOGO/AFP/Getty Images

Shugaban mulkin sojan kasar Mali Kanal Assimi Goita, ya amince da yin afuwa ga daukacin sojojin kasar Ivory Coast su 49 da kamen da aka yi musu a watan Yulin bara ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin kasashen biyu, kakakin gwamnatin Bamako Abdoulaye Maiga ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’ar da ta gabata.

Gwamnatin Mali ta kama sojojin da ta kira sojojin haya, bisa zarginsu da shirya makarkashiya da kuma yin zagon kasa ga  tsaron kasar mai fama da tashe-tashen hankula daga mayakan jihadi, inda daga bisani ta zartas musu da hukuncin dauri na shekaru ashirin, sai dai gwamnatin Ivory Coast da ma Majalisar Dinkin Duniya sun musanta zargin, suna masu cewa, sojojin sun shiga Mali ne da zummar dafa wa rundunar wanzar da zaman Lafiya da Jamus ta tsugunar a kasar don tabbatar da zaman lafiya a Mali.