1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali ta soke bikin ranar samun 'yancin kasa

Binta Aliyu Zurmi
September 14, 2023

Gwamnatin mulkin sojin kasar Mali ta sanar da soke shagulgulan zagayowar ranar samun yancin kasa da ke tafe a makon gobe bisa karuwar ayyukan 'yan ta'adda.

Mali | Colonel Assimi Goita
Hoto: Malik Konate/AFP

A sanarwar majalisar ministocin kasar ta ce Kanal Assimi Goita ya umurci yin amfani da kudin da aka ware domin wannan biki wajen tallafawa iyalan da ayukan 'yan ta'addan kasar ya shafa.

Kasar Mali tun a shekarar 2012 ta ke fama da hare-haren yan ta'adda wadanda ke da alaka da kungiyoyin al-Qaeda da IS.

Karin bayani: Soji hudu sun rasa ransu a Mali

Rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya Minusma wacce ke taimakawa a yakin da Mali ke yi da 'yan ta'addar bayan kwashe shekaru 10 ta kammala aikinta a kasar kamar yadda sojojin kasar suka bukata.

Mali ta sami 'yanci daga Turawan Faransa a ranar 22 na watan Satumba a shekarar 1960.