1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mali ta jaddada ficewa daga ECOWAS

Suleiman Babayo AMA
July 9, 2024

Ministan harkokin wajen kasar Mali ya kawar da yuwuwar sake komawa cikin kungiyar ECOWAS/CEDEAO, duk da matakin kungiyar na neman ganin an sasanta tsakanin bangarorin biyu.

Amirka, New York | Majalisar Dinkin Duniya | Mali Abdouaye Diop
Ministan harkokin wajen Mali, Abdoulaye DiopHoto: Mary Altaffer/AP Photo/picture alliance

Ministan harkokin wajen Mali, Abdoulaye Diop ya jaddada ficewar kasarsa da Burkina Faso gami da Jamhuriyar Nijar daga cikin kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS/CEDEAO, duk da matakin neman sasantawa da kungiyar take yunkuri.

Shugabannin kasashen uku a karshen wannan makon da ya gabata suka tabbatar da matakin fita daga cikin kungiyar ECOWAS tare da nasu kawancen. Ministan harkokin wajen na Mali ya ce kasarsa tana shirye da ci gaba da hadin kai da kungiyar ta ECOWAS. Sannan ya soki duk wani mataki na kakaba visa tsakanin kasashen uku da ECOWAS, sannan ya ce ficewar daga cikin kungiyar na da nasaba da zargin cewa kungiyar ta ECOWAS ta zama 'yar amshin shata na Faransa.