1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin juyin mulki a Mali ya ci tura

May 18, 2022

Mali, kwanaki uku bayan da gwamnatin mulkin soji ta ce ta dakile wani yunkurin juyin mulki, har yanzu ba ta yi karin haske kan gungun hafsoshin da ake zargi ba.

Sojojin Mali
Sojojin MaliHoto: Nicolas Remene/Le Pictorium/MAXPPP/dpa/picture alliance

Gwamnatin mulkin sojin Mali ta jadadda cikin wata sanarwa cewa, dakarun da suka yi yunkurin juyin mulkin sun samu goyon bayan wata kasa ta Yammancin duniya, ba tare da yin karin bayani ba. Amma dai ana ganin cewa fadar mulki ta Bamako tana zargin tsohuwar uwar gijiyarta Faransa da neman kawo karshen mulkin Hassimi Goita sakamakon tsamin dangantaka da aka samu tsakanin sassa biyu. Sai dai Aboubacar Sidick Fomba, na jam'iyyar APDM, ya ce wannan yunkurin ba zai kawo cikas ga hadin kan sojojin Mali ba."A gaskiya, Kanar-kanar biyar ne da suka hada da na sojojin sama, da na kasa, da masu tsaron kasa, da na 'yan sanda da kuma na Jandarmomi. Don haka daukacin bangarorin da ke tafiyar da rundunar sojin Mali ne suka dunkule a wuri guda. Ya tabbata cewa dakile wannan juyin mulkin na nufin cewa akwai hadin kai. Ba za a iya hana wasu mutane yin hadin gwiwa a matakai dabam-dabam ba. Wannan yunkurin ba ya kawo cikas ko kadan ga hadin kan sojojin. Dama na sanar tuntuni, Faransa ta bayyana karara cewa ba ta amince da gwamnatin mulkin soja ba, kuma za ta yi duk mai yiwuwa don kawo wa gwamnatin rikon kwarya karar tsaye."

Wadanda suka yi yunurin juyin mulkin sun ce sun samu goyon bayan wata kasa

Shugaban Kasar Mali Assimi Goita, Hoto: AP Photo/picture alliance

Sai dai ana ta cece-kuce kan hakikanin gaskiya wannan yunkurin juyin mulki, wanda ke zama na biyu cikin kasa da shekaru biyu a Mali kuma a tsakiyar matsalar ayyukan ta'addanci da yankin Sahel ke fama da shi. Sannan wannan dambarwar ta zo a daidai lokacin da abokan huldan Mali biyu wato Faransa da Rasha ke takun saka a yakin Ukraine. Abdoulaye Guindo, na hadakar Benbere, ya yi imanin cewa rashin kyakkyawan shiri ne ya sa wannan yunkurin ya ci tura . Amma ya nemi sojojin da ke mulki da kada su yi watsi da bukatun sojojin da ke akwai, amma su sauraresu da kunnuwan basira."Idan da kaso mai yawa na sojoji ne, da an ji karar harbe-harbe a ko'ina, da an ji karar hare-hare. To amma idan aka yi la'akari da cewa an murkushe yunkurin juyin mulkin ba tare da an yi harbi ko daya ba, hakan na nufin ba wani babban kaso na rundunar ba ne, wasu kebabbun sojoji ne. Don haka a gare ni, wannan yunkurin ba zai haifar da rarrabuwar kawuna tsakanin sojojin ba. Amma tilas ne mahukuntan na yanzu su ci gaba da yin magana da dukkanin rundunonin, don fahimtar abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya, wai shi mene ne abin da ba a cimma ba, sannan su yi aiki don ganin mun magance su, ta yadda za a karfafa wannan hadin kai a tsakanin jami'an tsaronmu."

An kame wasu manyan hafsoshin sojin guda biyar wadanda ake zargi da kitsa juyin mulkin

Sojojin MaliHoto: Nicolas Remene/Le Pictorium/MAXPPP/dpa/picture alliance

Sashen hulda da jama'a na rundunar sojojin Mali ya sanar da cewa a bata lokacin domin bayar da cikakken bayani kan binciken da aka fara gudanarwa bayan yunkurin juyin mulkin. Sai dai tuni aka kama wasu jami'an sojoji bakwai ciki har da hapsoshin sojoji biyar da ake zargi da hannu a yunkuri. Idan za a iya tunawa dai, gwamnatin mulkin sojin Mali ta juya baya ga kasar Faransa da kawayenta, tare da rungumar kasar Rasha a kokarin dakile yaduwar jihadi da ya yadu zuwa makwabciyarta Burkina Faso da Nijar.