Mali: Yan Jarida sun nemi a saki Alhousseini Togo
April 15, 2025
Alhousseini Togo ya wallafa wani rahoto a ranar 8 ga watan Afrilun 2025 mai taken "Tsarin shari'a na Mali ko matsalar karni, kuskuren Minista Mamoudou Kassogue". A cikin wannan labarin dai, jaridar "Canard de la Venise" ta nuna shakku kan sahihancin tsarin shari'a na alkalan kasar Mali, wadanda ya bayyana a matsayin "masu cin hanci da rashawa". Wannan caccakar ce ta bude kofar babban gidan yarin tsakiyar Bamako ga Alhousseyni Togo.
Dan jaridan na Mali ya fito karara wajen yin tir da rashin 'yancin cin gashin kai na bangaren shari'a tare da nuna shakku kan alkaluman da ministan shari'a Mamoudou Kassogue ya wallafa, wadanda ke bayyana cewa sama da kashi 70% na al'ummar kasar Mali sun nuna gamsuwa da tsarin shari'ar kasar.
A cewar Bandjougou Danté, shugaban cibiyar aikin jarida ta maison de la presse, wanda a 'yan makonnin da suka gabata ya yaba wa sojojin da suka hau kan karagar mulki a watan Agustan 2020 cewa babu wani dan jarida da suka daure, a yanzu kuma ya ce kamawa da kuma tasa keyar daraktan jaridar Canard de la Venise ya saba wa ka'ida da kimar da kwararrun kafafen yada labarai ke karewa.
"Abubuwan da muka dauka a matsayin matakai, a matsayin alkiblar da za mu dosa, kuma muke fatan wadannan yunkurin za su yi nasara. Ba nufinmu ba ne mu rura wuta ba saboda ba a samu salwantar rai ba, amma mun fuskanci wani bakin tabo a rayuwar sana'armu ta aikin jarida da kuma matsayar da muke karewa har izuwa lokacin da aka tsare wannan abokin aikinmu. Ba mu yi karya ba a lokacin da muka ce babu dan jarida da ke gidan yari. Sannan, mu yi abin da ya kamata a game da abin da ya shafi Aliou Touré, kuma lamari ne na sace mutane."
Shi dai Aliou Touré, dan jarida ne dan kasar Mali, babban editan na jaridar Le Democrate, wanda wasu 'yan bindiga dauke da makamai suka yi garkuwa da shi a ranar 6 ga Afrilu 2023, kafin a sake sako shi cikin koshin lafiya bayan wasu 'yan kwanaki. Amma dangane da Alhousseini Togo da ke tsare ba tare da shari'a ba, manyan kungiyoyin 'yan jaridu na kasar Mali sun bayyana rashin amincewa da kama shi saboda suna ganin cewa dan jaridar ya bayyana ra'ayinsa ne kawai kan yadda tsarin shari'ar kasar Mali ke gudana.
Marubuciya Fatouma Harber, wacce aka fi sani da Tinbuktu Woye, ta ce daure editan jaridar Canard de la Venise a gidan yari a yanzu na zama babbar barazana ga 'yancin fadin albarkacin baki a Mali.
"Wai shin muna da 'yancin tofa albakacin bakinmu a kan dukkan batutuwan da suka shafi abin da ya gudana a cikin kasar nan ko ma a duniya? Wannan yana da muni a matsayin masu bayyana ra'ayi ta yanar gizo da kuma 'yan jarida. Wannan tambayar mun baje ta a faidfai kuma tana tada damuwa sosai. Dama, akwai masu kaffa-kaffa a duk lokacin da za su rubuta rahoto domin suna gudun fitina a aikinsu. Sai dai baya ga wannan, akwai damuwa da ta zo ta karu a kai."
Wani abin damuwa shi ne sanya dan jarida Alhousseini Togo a gidan yari a karkashin dokar da ta shafi aikata laifuka ta yanar gizo, maimakon a karkashin dokokin da suka shafi laifuffukan a aikin jarida da aka kafa a shekara ta 2000, wadanda ba su dauke hukunci kan laifukan da 'yan jarida za su aikata ba.
A ranar 12 ga watan Yunin 2025 ne za a fara sauraren shari'ar dan jarida Alhousseini Togo na Mali.