Mali za ta mutunta yarjejeniyar Algiers
February 16, 2023Talla
Wannan mataki ya biyo bayan tangal-tangal da yarjejeniyar ke yi sakamakon aniyar 'yan twayen Azawad na yin fatali da ita, duk da kokarin da kasashen Afirka ke yi don shiga tsakanin bangarorin biyu da ke gaba da juna.
Tun a shekarar 2015 ne gwamnatin Mali da 'yan tawaye suka amince a kasar Aljeriya da kawo karshen yunkurin raba kasar gida biyu, sai dai ci gaba da gwabza fada da 'yan tawayen ke yi ya bazu zuwa tsakiyar Mali da kasashen Nijar da Burkina Faso da ke makwabtaka.
Gwamnatin sojin ta Mali ta ce sojojinta na shirin dawo da yankin Kidal da ke hannun 'yan tawaye na CMA a karkashi ikonta.
Amma a halin yanzu hukumomin Aljeriya na kokarin shawo kan bangarorin na Mali da ba sa jituwa da su kai zuciya nesa.