An amince da karbar bakin haure a Malta
June 7, 2020Talla
Daukacin bakin hauren 425 an ceto su da jiragen agaji, kana sun fito ne daga kasar Libiya, a cewar wata sanarwa daga hukumomin Malta suka fitar. Tun daga farko tsibirin Malta ya bukaci wasu sauran kasashen Turai da su karbi wani bangare na daga cikin bakin hauren, lamarin da ya ci tura har kawo zuwa yanzu, abinda hukumomin tsibirin suka yiwa kakkausar suka.
Akalla bakin haure 3.405 ne suka sauka a tsibirin bayan sun ratso teku daga Libiya a shekarar bara, adadin da yanzu hakan wasu fiye da 2.790 ke ci gaba da kasancewa a tsibirin, kana daga farkon wannan shekarar zuwa yanzu akalla bakin haure 1.400 ne suka yi kasadar zuwa kan tsibirin daga Libiya.