Mamakon ruwan sama ya kashe mutane a Brazil
May 2, 2026
Talla
A Brazil, mutane a kalla shida ne suka mutu a cikin sa'o'i 48, yayin da dama suka rasa matsugannasu sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake tafkawa a jihohin Pernambuco da kuma Paraiba. Mamakon ruwan saman ya haifar da ambaliyar ruwa da kuma zaftarewar laka. Hukumar kare aukuwar bala'i ta kasar ta rika kunna karararwar gargadi har sau 22 a fadin kBrazil, sakamakon karfin ruwan saman da ke sauka.
Karin bayani: Shugaban Brazil ya nemi duniya ta magance sauyin yanayi
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Shugaba Luiz Inacio Lula da Silva ya ce gwamnati za ta ci gaba da sanya ido kan iftila'in domin gaggawar kai dauki inda ake bukata.