SiyasaAsiya
Mamakon ruwan sama ya yi ta'adi a Japan
August 14, 2026
Talla
Akalla mutane hudu sun mutu a gabashin birnin Tokyo fadar gwamnatin Japan, sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da suka sauka a ranar Alhamis, kamar yadda mahukuntan yankin suka sanar a safiyar Juma'a.
Ambaliyar ta haddasa katsewar lantarki a gundumar Chima da ke gabashin Tokyo tare da dakatar da zirga-zirgar motoci da jiragen kasa, da kuma barin dubban mutane a makale a babban filin jirgin sama na Narita.
Hukumar kula da bala'o'i ta Chiba ta ce tana fargabar a samu karin mutanen da lamarin ya ritsa da rayukansu, yayin da ake ci gaba da neman wadanda suka yi batan dabo.
Hukumar ta kara da cewa i zuwa wayewar yau kusan gidaje 26,000 ba su da wutar lantarki, yayin da fiye da mutane 6,000 ke makale a filin jirgin sama na Narita.