1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiTurai

Turai: Ceto daga matatar man Dangote?

April 24, 2026

Matatar mai ta Dangote ta kafa tarihi, inda ta tura sama da lita miliyan 1000 na man jiragen sama zuwa Tarayyar Turai da nufin ceto sufurin saman da ke fuskantar barazana a halin yanzu.

Najeriya | Makamashi | Man Fetur | Aliko Dangote | Turai | Ciniki
Alhaji Aliko Dangote mamallakin matatar mai ta Dangote a NajeriyaHoto: Adam Abu-bashal/Anadolu Agency/picture alliance

Cikin kiddidigar da ke kasa yanzu, nan da sati shidan da ke tafe man jiragen sama ka iya karewa a daukacin Tarayyar Turai, sakamakon rikicin Amurka da Iran da ya kai ga rage yawan man da jiragen Turan kan samu da kusan kaso 50 cikin 100 a halin yanzu. Abun kuma da ya tayar da hankalin kamfanonin jiragen da ke fafutkar neman mafitar rikciin mai tasirin gaske, har ga tattalin arzikin Tarayyar Turan. Ya zuwa yanzun dai matatar Dangote na zaman ta kan gaba, a kokarin kai dauki zuwa jiragen Turan.

Dauki daga Dangote

Kimanin tan 876,000 ko kuma lita miliyan 1100 na man jiragen ne dai, Dangoten ya tura zuwa kasashen Turan a tsakanin watan Maris na jiya zuwa Afrilun da muke ciki. Dauki mafi girma kuma babban ceto ga kamfanonin jiragen, wadanda tuni suka fara tsayar da zirga-zirga zuwa hanyoyi dabam-dabam cikin neman rage zukar man. Kamfanin Lufthansa da ke zaman mafi girma a daukacin Tarayyar Turan dai ga misali, ya soke tashin jirage kusan 20,000 a cikin bazarar da ke tafe.

Najeriya: Ko matatar Dangoto za ta taimaka?

02:51

This browser does not support the video element.

Kyaftin Bala Jibril kwarrare ne a cikin sufurin na sama, kuma ya ce Dangoten ya daga darajar Najeriya da ma kimarta. Kamfanin Dangoten dai, na zaman na farko daga Tarayyar Najeriyar da ke tace makamashi yana kai wa Turai, a shekaru marasa adadi. Duk da arzikin man fetur dai, Najeriyar ta share lokaci tana zama 'yar kallo a kokairn cin gajiyar albarkarsa sakamakon gaza ta ce shi kafin kafa matatar da ta sauya da dama cikin siyasar makamashin da ke kanshin dan goma a yanzu.

Mafarki ya zamo gaskiya?

Ko bayan suna da kila ma kimarta dai, fitar man jirgin da ma ragowar makamashin da yake sarrafawa ya saka Dangoten zama na kan gaba a samar da dalolin da Najeriya ta dade tana ta mafarki. Matakin kuma da ke iya daga darajar ita kanta Naira ta kasar, ko bayan inganta tattali arzikin al'ummarta. Ya zuwa yanzun dai Dangoten ya bayyana aniyarsa ta sake kafa wata sabuwar matatar a kasar Tanzaniya, a wani abun da ke nuna alamun mayar da daukacin nahiyar zuwa ga dogaro da makamashin. Kasashen na Afirka dai, sun share lokaci suna ta dogaro ga kasashen Turan cikin batun makamashin mai tasiri ga tattalin arziki da ci-gaban al'umma.

Edited & Published by Lateefa Mustapha Ja'afar

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani