1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka a Jaridun Jamus: Turai na nuna sha'awar man Najeriya

Abdoulaye Mamane Amadou
July 15, 2022

A sharhunan da suka rubuta a wannan mako jaridun Jamus sun duba yadda nahiyar Turai ke ci gaba da nuna sha'awar albarkatun mai daga tarayyar Najeriya

Symbolbild | Nigeria Gaspipeline
Hoto: Florian Plaucheur/AFP/Getty Images

A sharhinta mai taken bututun alheri Mujallar Handeslblatt ta ce babu wata kasa a Afirka da ke da dumbin albarkatun mai kamar Najeriya. Ba da jimawa ba za a shimfida bututun da zai dauki mai mai tarin yawa zuwa nahiyar Turai in banda halin kunci da kasar ke ciki.

Kokari na diflomasiyya na cigaba domin cimma wannan manufa yayin da ake baiyana fargaba idan bukatar gaggawa ta taso. Ita dai kungiyar tarayyar Turai ta na bukatar samun man daga Najeriya domin rage dogaro akan kasar Rasha.

Da farko jakadun kasashen Italiya da Portugal da Spain da Faransa da ma kungiyar tarayyar Turan, sun kai ziyara kamfanin mai na Najeriya. Babbar tambayar ita ce mene ne yawan iskar gas din da Najeriya za ta fitar a nan gaba da zai zaburar da nahiyar Turai?

Najeriyar dai Allah ya huwace mata dumbin albarkatun mai shimfide a kasa, hasali ma ita ce kasa ta biyu da ke kan gaba a Afirka wajen fitar da gas zuwa kasashen waje bayan kasar Algeria.

Karin bayani: Yadda Afirka ta nemo yadda za ta samu alkama ya ja hankalin jaridun Jamus

Abin da ya sa nahiyar Turai ta ke ci gaba da nuna sha'awar man daga Najeriya shi ne sabanin sauran kasashe masu albarkatun man, Najeriya na da ingantaccen tsari na tura man mai tarin yawa.

Shirin shimfida bututun mai tsawon kilomita 4000 da zai ratsa ta sahara zai taso daga yankin Niger Delta zuwa Algeria inda kuma daga nan zai hade da wasu bututun da za su dauki man cikin sauki ta karkashin tekun bahar maliya zuwa nahiyar Turai.

Tambarin Kungiyar Tarayyar AfirkaHoto: Ludovic Marin/AFP/Getty Images

A sharhinta Jaridar Neuer Zürcher Zeitung ta yi tsokaci ne kan kungiyar tarayyar Afirka wadda ta ce ta kasance kurar baya a tsarin fasalin da ta dauka irin na kungiyar tarayyar Turai. 

Jaridar ta ce a bisa manufa ya kamata kungiyar tarayyar Afirka AU ta kawo karshen yake yake da habaka cigaban tattalin arziki a nahiyar amma shekaru 20 bayan sauya mata suna, cigaban bai taka kara ya karya ba.

A lokacin da aka kaddamar da sauyin sunan kungiyar shekaru 20 da suka wuce, an yi ta doki da murna, dubban jama'a da suka hallara a filin kwallon kafa na Durban a Afirka ta kudu sun yi ta shewa da jinjina.

Karin bayani: Rikicin Mali da Zambiya da yakin Ukraine sun dauki hankalin jaridun Jamus

Shugaba Thabo Mbeki wanda ya gaji Mandela ya yi jawabi yana mai cewa lokaci ya yi Afirka za ta dauki matsayinta a dangantakar kasa da kasa. Lokaci ya yi da za a kawo karshen mayar da Afirka saniyar ware.

Kungiyar hadin kan Afirka OAU wadda aka kafa a shekarar 1963, an yi amannar cewa ita da kanta ta zubar wa kanta kima da daraja. Ta tsaya kan manufar 'yar ba ruwanmu. ba za ta shiga al'amarin da ya shafi wata kasa mai cin gashin kanta ba.

Sai dai bayan kisan kare dangi da aka yi a Rwanda a 1994, dattawan Afirka suka rika zargin juna kuma a nan jakadu suka yarda cewa manufar kin tsoma baki ba zai yiwu ba.

Jaridar ta Neuer Zürcher Zeitung ta ce ya kamata kungiyar tarayyar Afirka AU ta yi kokarin magance matsaloli da suke tasowa a nahiyar ta bunkasa kawancen cinikayya da kuma samun karin martaba a siyasar duniya. Kungiyar tarayyar Turai EU wadda ta kwaikwaya ta yi kokarin samar da zaman lafiya a yankin arewacin Afirka da habaka tattalin arziki.

Yayin da AU ta fara da aklawura manya manya, a yanzu shekaru ashirin baya, tana waiwaye da tuntube.