Manafort zai bai wa kotun Amirka hadin kai
September 14, 2018Tsohon darektan yakin neman zaben shugaban Amirka Donald Trump wato Paul Manafort ya amince da laifin da kotu ke tuhumarsa da aikata na hada kai da wasu don cin amanar kasarsa, kuma ya yarda da yin aiki da mai gabatar da kara Robert Mueller a kan binciken zargin Rasha kan kutsen zabe.
Manafort mai shekaru 69 da haihuwa ya rigaya ya amince tun a watan Agusta da laifin zambatar baki cikin aminci da kin biyan haraji a wata shari'a da ta gudana a jihar Virginia. Wannan mika wuya na tsohon mai dasawa da shugaban na Amirka zai sa ya kauce wa hukuncin mai tsanani, wanda kuma ka iya shafa wa Trump kashin kaji makonni kalilan kafin zaben 'yan majalisa na tsakiyar wa'adinsa na mulki.
Fadar mulki ta White House ta yi gaggawar tabbatar da cewa shawarar da Paul Manafort ya yanke ba ta da nasaba da "shugaban Amirka da kuma yakin neman zabe da ya ba shi nasara a shekarar 2016". Dama shugaba Trump ya fada cewa ana tuhumar Manafort ne domin yi masa bita da kullin siyasa.