1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Manchester United ta lashe gasar kofin kalubale na Ingila

May 25, 2024

A gasar cin kofin kalubale na kasar Ingila wato FA Cup kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta lashe gasar, bayan doke babbar abokiyar hamayyarta Manchester City da ci 2 da 1, a wasan karshen da aka fafata.

Hoto: Kirsty Wigglesworth/AP/picture alliance

Duk da wannan nasarar da Manchester United  ta samu, galibin jaridun Ingila sun rawaito cewa akwai yuwuwar korar Erik ten Hag, mai horasa da kungiyar sakamakon rashin tabuka abin kirki a kakar wasa da ta kare.

Karin bayani: Tarihin Manchester United 

To sai dai a wasan da aka fafata a filin wasa na Wembley da ke Landan, akwai yiwuwar sauya matsaya dangane da wannan gagarumar nasara da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta lallasa abokiyar adawarta Manchester City .