1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane miliyan 6.5 sun sauke manhajar

Zainab Mohammed Abubakar
June 18, 2020

Mutane miliyan 6.5 suka sauke sabuwar manhajar zamani da za ta taimaka wajen gano cutar coronavirus a nan Jamus, cikin tsukin sao'i 24 da suka gabata.

Würzburg | Frau mit Mundschutz guckt auf Ihr Handy
Hoto: picture-alliance/HMB Media/H. Becker

Christian Klein ya bayyana cewar, yadda mutane suka yi maraba da wannan shiri, na nuna nasarar hadakar tawagar kamfanin na SAP da na sadarwar Jamus watau Deutsche Telekom, wanda ya kai ga samar da marhajar cikin makonni shida kacal.

Jamus ta hade da sauran kasashen Turai kamar Italiya da Poland da Latvia, wajen kaddamar da manhajar, ta hanyar amfani da Bluetooth wajen gano mu'amalar mutane, tare da yin gargadi idan daga bisani an gano wani  daga cikinsu na dauke da COVID 19.