Maniyatta sun hallara birnin Makka
July 17, 2021![Weltspiegel 10.05.2021 | Corona | Saudi-Arabien Mekka | Gebet mit Abstand](https://static.dw.com/image/57481884_800.webp)
Talla
Manyan motocin safa-safa ne su ka kawo maniyatan babban masalacin birnin mai tsarki inda suka fara da Dawafi, sai dai mutane dubu shida ne aka amince su yi dawafin a lokaci guda, sai bayan sun kammala sannan wasu su shiga.
Wannan dai shi ne karo na biyu ana gudanar da aikin hajjin tun bayan barkewar annobar ta Corona ko COVID-19. A bana mutane dubu sittin ne kacal wadanda aka yi wa rigakafin cutar mahukuntan Saudiyya suka amince su gudanar da aikin a maimakon sama da miliyan biyu da ke gudanar da aikin a baya.