1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Manoma a Jamus za su yi boren adawa da cire musu tallafi

Zainab Mohammed Abubakar
January 24, 2024

Manoman Jamus na shirin gudanar da zanga-zanga, a wani mataki na matsin lamba ga gwamnatin hadin gwiwa da Olaf Scholz ke jagoranta, da ta janye shirin rage tallafin man dizel na bangaren noma.

Hoto: Christophe Gateau/dpa/picture alliance

Manoman da suka fusata sun shafe makonni suna zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matakin rage tallafin, inda a yawnacin garuruwa suka tare hanyoyi da hana zirga-zirga da Traktoci da sauran kayan aikin gona.

Yanzu haka ana shirin gudanar da jerin gwanon motocin noma na trakta da gangami a birnin Mainz da ke yammacin Jamus, a yayin ziyarar mataimakin shugaban gwamnati kuma jigo a jam'iyyar kare muhalli ta The Greens Robert Habeck.

Masu shirya zanga-zangar suna sa ran taraktoci 500 zuwa 1,000 za su shiga zanga-zangar ta birnin Mainz. Kazalika ana shirin yin karin gangamin manoma a ranar Juma'a da ke tafe a jihar Lower Saxony da ke yankin Arewa maso Yammacin Jamus.