1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MANUFAR FARFADO DA TATTALIN ARZIKIN LIBIYA.

YAHAYA AHMEDApril 28, 2004

Bisa dukkan alamu dai, shugaban Libya Muammar al-Gaddafi, ya sake samun karbuwa da kuma amincewar gamayyar kasa da kasa. Game da hakan ne kuwa ya kawo ziyara a cibiyar Kungiyar Hadin Kan Turai da ke birnin Brussels na kasar Belgium, a ran talata da ta wuce. A cikin `yan makwannin da suka wuce ne kuma, Firamiyan Birtaniya, Tony Blair, ya kai masa ziyara a birnin Tripoli. A halin yanzu dai, abin da Libyan ta fi bukata ne farfado da kafofin hako man fetur dinta.

Shugaban kasar Libiya, Muammar al-Gaddafi da Firamiyan Birtaniya, Tony Blair a birnin Tripoli.
Shugaban kasar Libiya, Muammar al-Gaddafi da Firamiyan Birtaniya, Tony Blair a birnin Tripoli.Hoto: AP

Tun shekaru 43 da suka wuce ne Libya ke sayad da man fetur zuwa kasashen ketare. A cikin farkon shekarun 1970 ma, kasar ta dinga hako garwa miliyan 3 da digo 3 na gurbataccen mai. Amma a hankali, sai shugaban juyin juya hali Muammar al-Gaddafi, ya bijire wa kasashen Yamma. Game da hakan ne kuwa a cikin shekarun 1980, shugaban Amirka na wannan lokacin, Ronald Reagan, ya katse duk huldodi da Libyan. Takunkumin da Amirka da kuma Majalisar Dinkin Duniya, suka sanya wa Libyan a cikin shekarun 1990, ya janyo wa kasar asarar kudaden shiga na kimanin dola biliyan 18.

A halin yanzu dai, masana’antar man fetur ta kasar Libiyan na bukatar masu zuba jari daga ketare, don ta iya tsayawa sosai kan kafafunta. Kamfanoni da dama dai na nan na jiran samun izinin fara harkokinsu a Libiyan, bayan janye takunkumin da aka sanya mata, da kuma kusantar da ta yi da kasashen Yamma. Tuni dai, kamfanonin hakon man fetur kamarsu Repsoil na kasar Spain, da Statoil na Norway, da Occidental and Marathon na Amirka da kuma Agip na Italiya, duk sun fara shirye-shiryen komawa Libiyan, saboda suna ganin irin riba mai tsokar da za su samu a can. Ties Tiessen, wani manaja ne na reshen kamfanin Wintershall da ke Libyan, mallakar rukunin kamfanonin nan na BASF.

Ya bayyana dalilan da ya sa kasashen Yamma, suka fi nuna sha’awa ga man fetur din Libiya:-

"Man da ake hakowa a Libiya, mai ne ingantacce. Ba ya kunshe da yawan farar wuta. Matatan mai da yawa dai sun fi gwammace wa irin wannan man. Kusantar Libiyan da kasuwannin Turai kuma, ya sa jigilar manta zuwa kasashen Turan, ba ta da tsada. Bugu da kari kuma, kamfanonin hakon man sun fi samun riba da man Libiyan fiye da sauran man da suke hakowa a wasu wurare na duniya."

Babu shakka, nahiyar Turai dai, ita ce muhimmiyar abokiyar huldar Libiyan a kasuwancin man fetur. A ko wace shekara, nahiyar kadai na amfani da tan biliyan 12 na man fetur. Duk da cewa a wasu yankunan nahiyar ana hako man, har ila yau dai ta dogara ne kan man da ake samowa a Gabas Ta Tsakiya. Amirka kadai ma tana amfani da kashi 25 cikin dari na duk man da ake hakowa a duniya. Bayan sake alkiblar da gaddafi ya yi dai, Amirkan ta fara nuna sha’awa ga man fetur din Libyan. Kamar yadda Tiessen ya bayyanar:-

"A halin yanzu, Libiya na hako yawan mai ne tsakanin garwa miliyan daya da digo 3 zuwa garwa miliyan daya da digo 5, a ko wace rana. Gurinta ne kuwa, ta kai ga hako garwa miliyan biyu a ko wace rana, a cikin dan gajeren lokaci nan gaba. Shirin komawa kasar da kamfanonin Amirka ke niyyar yi dai, ya zo daidai a lokacin da ake bukatarsu. Za su kawo sabbin fasahohi, su kuma farfado da tsoffin kafofin hako man da suke kula da su a da. Suna kuma niyyar zuba jari da yawa a kasar."

An dai kiyasci cewa, yawan man da Libyan ke da shi a halin yanzu a karkashin kasa, ya kai garwa biliyan 36. Kuma, ban da Aljeriya. Ita ce kasar da ta fi yawan albarkatun Gas a duniya. Har ila yau dai, akwai yankuna da dama na kasar Libiyan, inda ba a gudanad da binciken gano ma’adinan da suke da su ba. Sabili da haka ne dai, kamfanonin Yamma ke ganin cewa, shiga hulda da Libiyan zai kawo musu amfani mai yawan gaske, a cikin shekaru da dama masu zuwa nan gaba.