1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manufofin kungiyar tsaro ta NATO

September 15, 2011

Tushen girka NATO,burin da ta sa gaba, kasashe membobin NATO da kuma yankunan duniya inda ta aika sojojinta.

Sakatare Janar na NATO Anders Fogh Rasmussen.Hoto: AP

Kungiyar tsaro ta NATO ko kuma OTAN a faransance an girka ta ranar hudu ga watan Afrilu na shekara 1949.

Babban burin da NATO ta kuduri cimma a lokacin girka ta shine zama wata garkuwa ga kasashen Turai ta fannin tsaro a daidai wannan lokaci na karshen yakin duniya na biyu, wato ta kasance kariya ga duk kasashe membobinta, kokuma riga kafi ga fadawar kasashen cikin bila´in yaki, saboda haka nema daya daga cikin kudurorin NATO ya rubuta karara cewar, idan wata kasa a duniya ta kuskura ta kaiwa daya daga cikin membobin NATO hari, tamkar ta kai hari ga sauran kasashen, wato za su yi taron dangi domin maida martani.

Wannan kuduri tamkar hannunka mai sanda ne a kasashen Rasha da Jamus,wanda a lokacin ake zargin su da da burin kara samun angizo a kasashenTurai, bayan koma bayan da su ka samu lokacin yakin duniya na biyu.

Kasashen da su ka kirkiro NATO sun bada hujjar daukar matakin girka wannan kungiya,da kasawar Majalisar Dinkin Duniya na tabattar da tsaro a cikin duniya, saboda haka su ka ga ya zama wajibi su dauki matakan kare kansu da kansu daga barazanar da yakin da duniya ke fama da ita a lokacin.

Yawan kasashe membobin NATO.

Tushen girka NATO wasu kasasahen Turai ne guda biyar wato Beljiam,Faransa,Luxemburg Holland da Ingila wanda su ka rattaba wa wata yarjejeniya hannu da ka fi sani da suna yarjejeniyar Brussels, wannan kasashe guda biyar, sune su ka gama baki da Amurika da Kanada, da kuma wasu karin kasashen Turai biyar wato Italy,Danmark,Island, Nowe da Portugal.Wannan gungun kasashe 12 sune tushen girka NATO a shekara 1949.

To amma yanzu OTAN na da kasashe membobi har 28.

Banda kasahe 12 na farko an samu karin kasashe 16 wato Albaniya, Bulgariya,Croatiya,Jamhuriya Cheque, Estoniya,Jamus Girka, Letoniya,Lituaniya, Poland, Roumaniya, Slovakiya,Spain da Turkiya.

Wato mafi yawan kasashen dake karkashin angizon Rasha su zama memba a cikin NATO da kuma ita kanta Jamus wadda take-taken ne ma ya sa girka kungiyar.

Jamus ta zama memba cikin NATO a shekara 1955, wato lokacin Jamus na rabe gida biyu, bangaren yamma ce ta zama memba ba ta yankin gabas ba.

Wanan sune kasashe 28 daidai membobin kungiyar tsaro ta NATO.To amma dabra da wannan kasashe akwai wasu karin kasahen duk da cewar su ba membobi ne ba a mma su nan da huldodi da kungiyar.

Kasashen dake taimakawa NATO da kudade

Duk shekara NATO na kashe tsabar kudade kimanin euro miliyan dubu biyu.Kasafin kudi ya kasu gida biyu akwai kudaden da ake warewa domin aikin rundunonin soja, sannan kudaden harakokin gudanarwa.

Kasashe biyar su ke bada gudummuwa domin tafiyar da aiyukan NATO, na farko dai Amurika wadda ke bada kusan kashi 30 cikin dari, sannan Jamus na taimakawa da kashi kusan 20 cikin dari da kuma Ingila wadda ke taimakawa da kashi 11 ,2 cikin dari, ta hudu kasar Italie mai bada kashi 7,7 cikin dari sai kuma Faransa wadda ke taimakawa da kashi 7,5 cikin dari.

Yankuna duniya da NATO ta taba aika sojojinta.

NATO ta fara aika sojoji a gabar tekun kasar Yougoslabiya domin sa ido ga takunkumin sayen makamai da Majalisar Dinkin Duniya ta kargamawa kasar.Sojojin NATO sun yi wannan aiki daga shekara 1992 zuwa 1996.

Sai kuma a Bosniya daga shekara 1995 zuwa 2004, inda ta aika dakaru dubu bakwai domin taka burki ga kissan gillan ga jama´a.

Tsakanin watan Afrilu zuwa Ogusta nan shekara 1999 NATO ta aika sojojin dubu bakwai a Albaniya domin kariya ga mutane Kosovo da su ka yi gudun hijira Albaniya dalili da yakin da ya barke a yankin Kosovo.

Sannan a lokacin yakin na Kosovo NATO ta tura sojoji fiye da dubu 40.

Sai kuma kasar Afganistan inda yanzu haka ta ke da dakarunta wanda ke fafataka da yan Taliban.

Tun watan Ogusta na shekara 2003 NATO ta tura dakarunta a Afganistan.

Sannan daga shekara 2003 zuwa 2010, NATO ta aika sojoji a kasar Iraki.

Sojojin karshe da NATO ta aika ta tura su ne a kasar Libiya wanda suka taimakawa ´yan tawaye su ka kifar da shugaba Mohammar Khadafi.

Cibiyar NATO ta nan a birnin Brussels na kasar Beljiam tun 1966, amma babban comandan sojojin na da ofishinsa a wani birnin mai suna Mons wanda shima ke cikin kasar Beljiam.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Mohammad Nasiru Awal