1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar harshen uwa ta duniya

February 22, 2022

Muhimmancin kare kananan harsunan ta hanyar koya wa yara tun suna kanana, saboda barazanar bacewa da mamayen manyan harsuna.

Almajiri I Yara I Afirka ta Yamma
Koyar da yara harshen uwa na da matukar muhimmanci ga rayuwarsuHoto: DW/Katrin Gänsler

A yayin da ake bikin ranar harshen uwa ta duniya, kabilun al'ummar kadancin Kaduna da masu ruwa da tsaki a kan kare al'adun gargajiya sun fara bullo da dabarun kare kananan harshensu daga barazanar  bacewa, lamarin da ke sanya iyaye gazawa koya wa ‘ya'yan su harshensu  na gado.

To sai dai lokacin da ake bikin wannan rana ta duniya wanda kungiyar kyautata ilmi da kimiyya tare da al'adu ta MDD ta ware domin dai  a yunkurin bunkasa harsunan duniya don kare su daga barazanar bacewa.

A nan Najeriya dai harsuna da dama ne suka kama hanyar bacewa sakamakon auratayya tsakanin kabilu da yanayin shigowar zamani tare da kuma yadda iyaye ke kin kunya koyawa ‘ya'yan su harsunan na gado.

To sai dai a yankin kudancin Kaduna wasu kabilun sun fara bullo da dabarun kare kananan harsunansu ta hanyar dagewa koyawa ‘ya'yansu da kuma yadda wasu suka koma anfani da yanar gizo wajen yin manhajar koya wa ‘ya'yansu harsunansu na asali.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani