1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben share fage na jam'iyyun Najeriya ya kankama

October 2, 2018

Yanzu ta tabbata Muhammad Inuwa Yahaya zai yi taraka na gwamna a Jihar Gombe karkashin jam'iyyar APC haka ita PDP ta cire dan takara kuma labarin ke nan a sauran sassan Najeriya.

Nigeria Oppositionspartei APC
Hoto: DW/K. Gänsler

Ita ma jam'iyyar APC ta kammala na ta zaben inda aka zabi Muhammad Inuwa Yahaya wanda ya yi takara na gwamnan jihar Gombe karkashin jam'iyyar a zabukan shekara ta 2015.

A zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP mai mulki a Jihar Gombe inda Alhaji Bayero Nafada ya samu nasarar lashe zaben tsakanin ‘yan takara 13 da Kuri'u 1105. Zaben wanda aka gudanar da shi cikin tsauraran matakai na tsaro biyo bayan hargitsi da aka samu a ranar farko da tsara gudanar da zaben.

Hoto: DW

Jam'iyyar APC mai adawa a jihar ta Gombe ta kammala zaben lafiya inda Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya wanda ya yi wa jam'iyyar takara na gwamnan Jihar Gombe karkashin jam'iyyar a zabukan shekara ta 2015 ya samu nasara kan sauran mutune 8.

A wani takaitacen bayani da ya yi jim kadan bayan da aka sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin Alhaji Inuwa Yahaya ya nemi goyon sauran 'yan takara da su hada kai domin cimma nasarar kafa gwamnatin APC a jihar.

Daukacin sauran ‘yan takara a jam'iyyar APC sun yi alkwarin hada kai domin samun nasarar jam'iyyar kamar yadda Alh Habu Mu'azu daya daga cikin 'yan takara ya tabbatar.