Manyan jami'an diplomasiya na ci gaba da tattaunawa da Iran
April 2, 2015A wannan Alhamis ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif ya ce yana da kyakkyawan fata nan ba da jimawa ba Iran da kasashe shida da suka shiga tattaunawa da ita kan shirinta na nukiliya za su fid da wata sanawar hadin guiwa idan an cimma wata yarjejeniya kan warware takaddamar.
"Sanarwar za ta kasance ta manema labaru wadda abokanmu za su yi aiki kai. Amma ba mu san yadda za ta kasance ba domin har yanzu ana bukatar tattaunawa tsakanin kasashen shida kuma har yanzu ba mu san batutuwan da suke shawartawa kai ba. Amma da yardar Allah za a ba da sanarwar hadin guiwa da ni da wakiliyar tarayyar Turai Federica Mogherini da ke wakiltar wannan gungu."
Manyan jami'an diplomasiya na kasashe masu kujerun dindindin a Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya hade da Jamus na ci gaba da tattaunawa da kasar ta Iran a Lausanne da ke kasar Switzerland a kokarin cimma masalaha game da shirin nukiliyar gwamnatin Teheran.