SiyasaJamus
Manyan kasashe sun gargadi Sudan
January 5, 2022Talla
Kasashen Amirka da Birtaniya da Norway da ma Tarayyar Turai, sun gargadi jagororin soja a Sudan cewa ba za su goyi bayan nada sabon firaministan ba, sai har idan 'yan kasar ne suka aminta da shi.
Manyan kasashen na duniya, sun yi barazanar janye duk wani tallafin da suke bai wa Sudan, idan har sojojin suka yi gaban kansu wajen nada wani nasu a matsayin sabon firamnistan.
Wannan na zuwa ne sakamakon boren da 'yan Sudan ke ci gaba da yi na adawa da mulkin soja, bayan murabus da tsohon firaminista Abdallah Hamdok ya yi a ranar Lahadin da ta gabata.