Kasashe uku na sun sha alwashin sauyi a EU
June 27, 2016Talla
Shugabanni daga kasashen Faransa da Italiya da Jamus sun bayyana cewa za su dauki sabbin matakai na sake kullewa tsakanin juna inda za su ci gaba da ayyukan ci gaba tsakanin kasashe 27 na kungiyar EU bayan da Birtaniya ta dauki mataki na raba gari da kungiyar.
Bayanin hakan ya fito ne bayan da shugaba Merkel ta Jamus ta karbi bakuncin wadannan shugabanni na manyan kasashe uku da ke cikin wannan kungiya ta EU a birnin Berlin. Shugaba Merkel da Francois Hollande da Firaminista Matteo Renzi sun dai ce babu wata tattaunawa a hukumance ko ba a hukumance ba kan batun ficewar ta Birtaniya har sai an turo da bukatar neman barin wannan kungiya daga mahukuntan na Birtaniya.