1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Manyan kasashe za su taimaka wa Afghansitan

October 12, 2021

Shugabannin kasashe mafiya karfin tattalin arziki a duniya wato G20, na wani taro na musamman a wannan Talata da nufin bullo da dabarun maganta matsalolin Afghansitan.

Italien l G20-Treffen Neapel l Umwelt Klimapolitik l logo
Hoto: Fabio Sasso/ZumaWire/dpa/picture alliance

Taron wanda Italiya ke jagoranta, zai tattauna sabbin barazanar taddanci da na jin kai da ma yadda za a yi hulda da gwamnatin Taliban.

Al'amura dai sun kara rincabewa a Afghanistan tun bayan kwace iko da kungiyar Taliban ta yi a tsakiyar watan Agusta, bayan janyewar sojojin Amirka da sauran wasu na kasashen yamma da ke a kasar tsawon shekaru 20.

Gwamnatocin kasashen duniya na muhawara a kan yadda za a ceto kasar, inda zuwa yanzu akalla mutum miliyan uku da dubu 500 da suka rasa muhalli.

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ta nuna bukatar taron ya kawo karshen babbar matsalar jin kai da ta fito fili a Afghanistan din, a tattaunawarta da Firaministan Italiya, Mario Dragi.