1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manyan kasashen Turai sun ja hankalin Iran a kan takunkumi

September 28, 2025

Iran ta janye da jakadun ta daga kasashen uku zuwa Tehran domin yin shawarwari, matakin da ke da nasaba da barazanar takunkumi kan shirin nukiliyart.

Shugaba Masoud Pezeshkian na kasar Iran
Shugaba Masoud Pezeshkian na kasar IranHoto: Iranian Presidency/Anadolu/picture alliance

Kasashen Burtaniya da Faransa da Jamus sun yi kira ga Iran da kada ta kara tsananta rikici a dangane da batun nan nukiliyarta, maimakon hakan a nemi sulhu ta hanyar tattaunawa, bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta sake kakaba wa ƙasar takunkumi a ranar Asabar.

Iran ta dawo da jakadun ta daga kasashen uku zuwa Tehran domin yin shawarwari, matakin da ke da nasaba da barazanar takunkumi kan shirin nukiliyart.

Kamfanin talabijin na gwamnatin kasar ya ruwaito cewa, dalilin wannan mataki shi ne halayen na kasashen uku, wadanda ke goyon bayan dawo da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya da aka soke.

Kafin wannan dai, galibin mambobin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya sun ki amincewa da kudurin da China da Rasha suka gabatar, wanda zai bai wa Iran karin lokaci domin tattaunawa.