Maraba da matakan yaki da Ebola
September 17, 2014Talla
Shugabar kasar Laberiya Ellen Johnson-Sirleaf ta yi maraba da sababbin matakan da Amirka ta dauka domin yaki da cutar Ebola mai saurin kisa, inda ta yi fatan cewa sauran kasashen duniya za su bi sahun Amirkan. A wata sanarwa da aka raba wa manema labarai, Sirleaf ta ce matakin tura sojoji domin taimakawa wajen yakar Ebola a kasashen da cutar ta addaba abin a yaba ne kuma wani namijin kokari ne. Laberiya dai ita ce kan gaba wajen asarar rayuka da ma wadanda suka kamu da cutar ta Ebola cikin kasashe hudun da suke fama da ita a yankin yammacin Afirka.