Jibril Aminu ya kafa tsarin ilimin makiyaya a Najeriya
June 6, 2025
Fitattaun 'yan siyasa da masu fada a Najeriya, na jaje kan rasuwar tsohon ministan ilimi da man fetur a kasar Prof Jibril Aminu, marigayin ya mutu yana da shekaru 85 bayan fama da jinya. An haifi marigayi Prof Jibril Aminu, a ranar 25 ga watan Agusta na shekarar 1939 a karamar hukumar Song da ke Jihar Adamawa. Ya je Barewa kwaleji da ke Zariya, kafin ya kware a matsayin likitan zuciya a digirinsa na farko a Jami'ar Ibadan a shekarar 1965.
Karin Bayani: Najeriya da dakatar da bai wa dalibai tallafin karatu a waje
Ya jagoranci kungiyar manyan malaman jami'o'in Najeriya NUC a 1975-79, sannan ya samu digiri na uku a fannin likitanci daga jami'ar Royal Post-Graduate Medical School da ke birnin Landan a shekarar 1972.
Marigayin ya taka rawa a siyasar Najeriya, inda ya zama Jakadan kasar a Amurka daga 1999 zuwa 2003, ya zama Sanata mai wakiltar Adamawa ta tsakiya daga 2003 zuwa 2011. Farfesa Jibrin Aminu ya zama shugaban jami'ar Maiduguri daga shekarar 1980 zuwa 85.
Najeriya ta yi babban rashin mai kishin kasa, abin koyi ga sauran 'yan siyasa a cewar Prof Abba Tahir. Marigayi Prof Jibrin Aminu, ya kawo wa Najeriya cigba a loakcin da ya yi ministan ilimi a shekarar 1989 zuwa 90, sannan ma'aikatar man fetur ta kasar ta shiga gogayya a duniya a loakcin da ya zama ministan harkokin mai daga 1990 zuwa 92.
Marigayin ya rasu a ranar Alhamis 5.6.2025 a wani asibiti a Abuja, bayan doguwar jinya yana da shekaru 85 a duniya, ya bar yaya 9, ciki akwai Bashiru Aminu da Murtala Muhammad Aminu, masana tattalin arziki da ‘yan kasuwa. Akwai mata. An yi salla ce shi a birnin tarayyar Najeriya, sannan a binne shi a karamar hukumar Girei da ke jihar Adamawa. Gwamnatin Adamawa ta fitar da sanarwar jaje ga iyalai da sauran 'yan kasa.