1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta karrama Mahsa Amini

Abdul-raheem Hassan
October 19, 2023

Kungiyar Tarayyar Turai ta ba da babbar lambar yabonta na "Sakharov Prize" ga marigayiya Mahsa Amini, 'yar kasar kasar Iran da ta mutu a hannun jami'an tsaro a shekarar 2022.

Masu zanga-zanga sun daga hoton marigayiya Mahsa Amini a dandalin Trafalgar da ke birnin LandanHoto: Jonathan Brady/PA Wire/empics/picture alliance

Sanarwar kyaututtukar EU na zuwa ne bayan da aka ba da lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel ga wata mai fafutukar kare hakkin dan Adam a Iran da ke daure mai suna Narges Mohammadi. "Ranar 16 ga watan Satumba mun cika shekara guda da kisan Jina Mahsa Amini a Iran. Majalisar Turai tana alfahari da tsayawa tare da jajirtattu waɗanda ke ci gaba da yaƙin neman daidaito, mutunci da 'yanci a Iran," inji Shugabar Majalisar Tarayyar Turai Roberta Metsola.

Amini ta mutu a ranar 16 ga Satumba, 2022 tana da shekaru 22 a duniya, 'yan sandan sun tsare ta bisa zargin keta ka'idojin tsarin shigar mata na jamhuriyar musulunci a Iran. Sai dai hukumomin kasar sun yi ikirarin cewa matashiyar ta mutu ne a gidan yari sakamakon wata rashin lafiyar da ba a bayyana ba. Matakin da ya haifar da zanga-zanga mai muni a ciki da wajen kasar. 

Tun daga shekarar 1988 Majalisar Tarayyar Turai ke ba da lambar yabo ta Sakharov ga daidaikun mutane ko kungiyoyi masu kare hakkin dan adam don karfafa 'yancin fadin albarkacin baki. A shekarar da ta gabata ne aka bayar da kyautar ga 'yan kasar Ukraine saboda yakin da suke yi da kasar Rasha. An shirya bikin bayar da kyautar na bana a watan Disamba na shekarar 2023.