Maroko ce zakara da Allah ya nufa da cara a U17 na Afirka
April 21, 2025
A karon farko kungiyar kwallon kafar Maroko ta matasa 'yan kasa da shekaru 17 da haihuwa ta lashe kambun gasar da ta dauki bakuncinsa tun daga ranar 30 ga watan Maris zuwa 19 ga watan Afrilun 2025, bayan da tayi kare jinni biri jinni da 'yan wasan kasar Mali da suka kai ga bugun daka kai sai mai tsaron gida. Wannan ya sa kasar ta Maroko ta taki sa'a da ta kaita ga zura kwalleye hudu a ragar Mali da ta taba lashe gasar sau biyu, wacce ita kuma ta zura kwallaye biyu kacal. Lashe gasar matasa 'yan kasa da shekaru 17 da Maroko ta yi, ya kara mata karfin gwiwa da fatan sake lashe kofin nahiyar Afirka Afcon da kasar za ta dauki bakuncinsa a bana.
Baya ga Maroko a matsayin farko da Mali a matsayi na biyu, Côte d'Ivoire ta samu matsayi na uku na gasar 'yan kasa da shekaru 17 da haihuwa na Afirka bayan da ta samu galaba a kan Burkina Faso da ci 4-1 a bugun fenariti.
Wainar da aka toya a gasar zakarun Afirka da ta confederation
Har yanzu dai muna Afirka, inda a karshe mako aka gudanar da matakin farko na wasan kusa da na karshe na neman lashe kofin zakaru na wannan nahiyar. Sai dai kungiyoyin da ake ji da su ba su zura kwallo ko da daya ba, inda Mamelodi Sundowns ta Afirka ta Kudu da Al Ahly ta Masar suka yi canjaras 0-0. Irin wannan sakamako 0-0 aka samu a karawa da daya wakiliyar Afirka ta Kudu Orlando Pirates da daya wakiliyar ta Masar Pyramids.
A gasar Confederation ta Afirka kuwa, kungiyar Simba SC ta kasar Tanzaniya ta samu nasara a matakin farko na wasan kusa da na karshe, bayan da ta doke Stellenbosch ta Afrika ta Kudu da ci 1-0. Sai dai a bangarenta, RS Berkane ta Maroko ta yi CS Constantine ta Aljeriya dukan kawo wuka (4-0), lamarin da ya ba ta damar fara jin kamshin wasan karshe a karo na biyu a jere. Dama, RS Berkane ce ta lashe confederation cup na Afirka a 2020 da 2022.
Kiris ya rage Bayern ta zama zakaran Bundesliga
A Jamus, kungiyar Leverkusen ta yi bankwana da fatanta na lashe kambun zakaran kwallon kafa na Bundesliga karo na biyu bayan da ta yi kunnen doki 1-1 da St. Pauli, lamarin da ke kara fadada wa Yaya-babba Bayern Munich hanyar sake zama gwana. A daidai lokacin da ya rage wasanni hudu a kammala kakar-wasan Bundesliga, Leverkusen ta da ratar maki takwas da Bayern wacce ra ragargaji Heidenheim da ci 4-0. koci Vincent Kompany da zaratan na Munich na bukatar maki biyar ne kawai don samun kambu na 34.
A nata bangaren, Eintracht Frankfurt ta kama hanyar samun cancantar shiga gasar zakarun Turai, duk da canjaras da ta yi a Augsburg 0-0, lamarin da ke ba ta damar zama ta uku da maki 52 a teburin Bundesliga. Su kuwa Leipzig da Kiel sun yi kunnen doki (1-1) yayin da Mainz da Wolfburg suka tashi 2-2. Ita kuwa Yaya-karama Borussia Dortmund ta yi nasarar doke Mönchengladbach da ci 3-2, lamarin da ya ba ta damar sake cike makin da ke raba ta da matsayi na hudu da take hari domin a dama da ita a gasar zakatun Turai saboda yanzu Dortmund na da maki 45 yayin da Leipzig ke da 49.
Inda aka kwana a manyan lig na kasshen Turai
Yanzu kuma sai sakamakon wasannin sauran manyan lig na kasashen Turai, inda a Spain, kwallon da Federico Valverde ya ci ya baiwa Real Madrid nasara mai mahimmanci a kan Athletico Bilbao da ci 1-0, lamarin da ya sa matar jiya kasa canza zani a teburin La Liga. Bayan makonni 32 na fara wasan La Liga, masu rike da kambun zakaran Spain na bayan FC Barcelona da tazarar maki hudu, wacce ita ma ta yi nasara a kan Celta Vigo da ci 4-3 a mintunan karshen wasa.
A Faransa kuwa, an harbi alkalin wasa na biyu a ka a lokacin wasan hamayya tsakanin Saint-Etienne da Lyon, wanda aka katse tsawon minti 45 a ranar Lahadi, a wani sabon cin zarafi da ya shafi kungiyar alkalan wasa a gasar Ligue 1. Sai dai daga bisani, an ci gaba da wasan ba tare da an samu matsala ba, kuma Saint-Etienne ta doke Lyon da ci 2-1. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomi ke barazanar rusa kungiyoyin magoya bayan Saint-Etienne guda biyu sakamakon tashin hankali. Dama dai Paris Saint Germain ta riga ta zama zakaran kwallon kafar Faransa tun makonni biyun da suka gudata.
A Italiya, Inter Milan ba ta da tabbacin ci gaba da rike kambunta na Serie A bayan da ta sha kashi a hannun Bologna da ci 1-0, sakamakon da ya bai wa Naples ko Napoli damar cike gibin maki da ke tsakaninsu bayan da ta doke Monza 1-0. A yayin da ya rage wasanni biyar a kawo karshen kakar wasa ta bana, Inter Milan da Napoli na da maki 71 kowannen su, amma Inter na saman teburi sakamakon yawan kwallayen da ta zura. Ita kuwa Atalanta ta karfafa matsayinta na uku da maki 64 ta hanyar nasara da ci 1-0 a San Siro a karawar da suka yi da AC Milan da ke a matsayi na tara.
Wasan tennis: Alcaraz da Zverev sun dauki hankali
Mako guda bayan nasarar da ya samu a Monte Carlo, Carlos Alcaraz da ke zama dan wasan tennis na biyu mafi shahara a duniya ya gaza lashe kofin gasar Barcelona sakamakon duka da ya sha a hannu Holger Rune da ci 7-6 (8/6), 6-2. A daidai lokacin da ya rage wata daya ya kare kambunsa a Paris, Alcaraz ya nuna kasala a farkon zagaya na biyu na wasan da ya yi da lambar 13 ta duniya. Sai dai kuma wannan kofin da ke zama na biyar ya kasance mafi kyau ga tarihin Holger Rune, dan kasar Denmark mai shekara 21 da haihuwa. Hasali ma, ya kawo karshen rashin nasara 13 da ya samu a gaban wadanda suke rike da matsayi daya zuwa biyar a fagen tennis.
A bangarensa, dan wasan Jamus da ke zama na uku a duniya Alexander Zverev ya lashe kofin gasar ATP na Munich sakamakon doke Ba'amurke Ben Shelton (lamba 15 a duniya) a wasan karshe da ci 6-2 da 6-4. Wannan dai shi ne karo na uku a tarihin rayuwar Bajamushen da ya lashe gasar Munich bayan 2017 da 2018, kuma na farko a matsayin ATP 500, da ke zama rukuni na uku na tennis bayan Grand Shlem da Master.