Kofin Duniya: Maroko ta doke Beljiyum
November 27, 2022!['Yan wasan Beljiyum na neman kwatar kwallo a hannun dan wasan Maroko](https://static.dw.com/image/63907252_800.webp)
Talla
A ci gaba da fafatawa a gasar cin kofin duniya, a wannan Lahadi, Maroko ta lallasa kasar Beljiyum da 2-0. 'Yan wasan Beljiyum wadanda suka zo na uku a gasar cin kofin duniya ta 2018 tun da farko sun so samun galaba a wannan wasa na yau da zai ba su damar zuwa mataki na gaba a rukunin F. To amma 'yan wasan Moroko Abdelhamid Sabiri da Zakaria Aboukhlal sun katse wa Beljium hanzari ta hanyar zura wa Turawan na Beljiyum kwallaye biyu a raga ana dab da tashi wasa.