1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaMaroko

Maroko ta yarda da agaji daga wasu kasashe

September 11, 2023

Hukumomi an Maroko sun yarde wa kasashe hudu kacal domin aike tawagogin jami'an agaji don ci gaba da laluben mutanen da ake kyautata zaton sun makale a karkashin gine-gine.

Erdbeben in Marokko
Hoto: Sylvain Rostaing/Le Pictorium/MAXPPP/dpa/picture alliance

Yayin da kasashen duniya ke tururuwa domin kai dauki ga Maroko bayan aukuwar ibtila'in girgizigar kasa a karshen makon jiya, hukumomin kasar sun sanar da amincewa su karbi tayin agaji daga kasheshe hudu kacal domin ci gaba da laluben mutanen da ake kyautata zaton sun makale a karkashin gine-gine.

Karin bayani: Maroko: Ana ci gaba da aikin ceto bayan girgizar kasa

A cikin wata sanarwa da ta fidda a jiya Lahadi ma'aikatar cikin gida ta Maroko ta bayyana cewa kasar ta amince wa kasashen Spain da Burtaniya da Qatar da kuma Hadaddiyar daular Larabawa da su aike tawagar jami'an agaji domin gudanar da aikin ceto yayin da tayin kasashen da dama ciki har da Faransa da Amurka da kuma Izra'ila ya gaza samun karbuwa.

Hukumomin na Moroko sun ce nan zuwa gaba za su duba yiwuwar ba da dama ga sauran kasashen domin kawo masu dauki a cikin wannan yanayi mai matukar wahala.

A daren Jumma'ar da ta gabata ne dai Maroko ta fuskanci ibtila'in girgizar kasar mai karfin maki 6.8 a ma'aunin Richter wanda kawo yanzo ya ritsa da rayukan mutane 2.100.