Taron Majalisar Dinkin Duniya a Maroko
December 10, 2018Gabanin kaddamar da taron da Majalisar Dinkin Duniyar za ta gudanar dangane da sabon shirin nata kan batun bakin haure da 'yan gudun hijira da za a gudanar a kasar Morokko, wakiliyar majalisar ta musamman Louise Arbour ta koka da matsalar yada labaran bogi kan shirin da aka yi wa lakabi da Migration Pact. Arbour ta nunar da cewa shirin bai zamo wajibi kan kowacce kasa ba, kasancewar ba doka ba ne kuma ba 'yanci ne aka bayar na yin hijira ka kowa ba.
Sama da kasashe 150 ne dai za su tattauna kan shirin na migration pact a birnin Marrakech na Morokko a wannan Litinin din. Daga cikin wadanda za su gabatar da jawabi a yayin taron da ke son sake tsarin makomar 'yan gudun hijira da kuma magance matsalar bakin haure da ke shiga kasashe ba bisa ka'ida ba, har da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.