1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kawo karshen rufe boda a Najeriya

Abdourahamane Hassane
December 24, 2020

Sakamakon bude kan iyakokin da Najeriya ta yi wanda aka kwashe sama da shekara guda suna rufe, ya janyo muhawara tsakanin masu tunanin an yi daidai da kuma masu kallon sake bude iyakar ka iya sake haifar da sabon rikici.

Nigeria Grenze zum Niger
Hoto: DW/Y. Ibrahim

Rufe iyakokin na Najeriya kafin a bude, a tsawon watani 16 gwamnatin na cewar ta cimma nasarori na rage yawan shigar makamai daga kassahe makobta da kuma ayyukan sarande. Sai dai akwai muhawara a tsakanin 'yan kasar a kan wannan batu yayin da wasu suke ganin tattalin arzikin Najeriya ya samu ci gaba wasu na ganin an wahala har ma da kasashe makobta. Mun tanadar muku rahotanni dangane da wannan batu.

 

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Rahotanni da Sharhuna