1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani dangane da furucin dakarun sojin Najeriya kan 'yan matan Chibok

May 27, 2014

Cece-kuce ya biyo bayan ikirarin dakarun sojin Najeriya na cewa sun san inda 'yan mata su ke, amma sai sun yi dammara na musamman za su iya kubutar da su

Nigeria Protest Boko Haram Entführung 26.5.2014
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Kasa da 'yan awoyi da bayyana gano wurin da 'yan mata 'yan makaranta na Chibok, ra'ayi na cigaba da banbanta a tsakanin masu ruwa da tsaki a cikin rikicin da suka ce kalaman sojojin sun kama hanyar kauce hanya.

Sun dai share makonni har kusan bakwai a dokar daji, kafin daga baya sojan kasar ta najeriya suce sun gano inda suke. To sai dai kuma daga dukkan alamu kalaman rundunar tsaron dake jagorantar yakin ya gaza kaiwa ga burge shugabannin al'ummar yankin da suke fadin gani a kasa na zaman karatu na karen da ake biki a gidansu.

Dattawan da a baya suka zauna suka yi Allah wadarai da rikon sakainar kashin da suke zargin mahukuntan kasar dayi a cikin rikicin dai sunce duk wani kalami a bangaren sojan kasar koma duk wani mai ruwa da tsaki da ceto yaran nan dai ba za su kai ga gamsar da al'ummar yankin ba a cewar Mallam Adamu Chiroma dake zaman shugaban kungiyar dattawan sashen Arewa maso Gabashin kasar da ke fama da rigingimu.

“ Na tabbata yanzu kowa a dame ya ke cewar ga kwanakin da yaran nan ke hannun miyagun mutane amma sai sabbabin kalamai ake da fadin abubuwan da ake zato zasu farantawa mutane, amma abun da mutane suke nema mai sauki a mayar da yaran nan a kwato su, sojojin ma saurin magana kawai sukai abun da kawai zasu yi su kwato su”

Dabarun kwato yara ko kuma siyasa da makomar yaran dai, sabon matsayin sojan kasar ta Najeriya na zuwa ne dai dai lokacin da kafofi masu zaman kansu ke ruwaito rushewar kokarin sulhu tsakanin gwamnatin da yan kungiyar ta Fafutuka.

A baya dai an rika hasashen yiwauwar sakin yaran bayan wani sulhun da wani dan jarida mai zaman kansa dan asalin yankin ke jagoranta da kuma a karkashinsa gwamnatin za ta kai ga musayar yaran da wau yayan kungiyar guda dari dake gidan yari daban daban cikin kasar.

Hafsoshin sojin Najeriya wajen gangamin neman sako 'yan matanHoto: picture-alliance/AP

Sulhun kuma da ya kai ga rushewa bayan da gwamnatin ta kai ga janyewa cikin awoyin karshe bisa hujjar adawarta da sulhu da kungiyar da take yi wa kallon ta ta'adda.

Burin al'ummar Arewa maso Gabashin Najeriya

To sai dai kuma a cewar Adamu Chiroman al'umm'ar yankin ba su damu da hanyar sulhu ko karfi ba face ganin 'ya'yansu a raye da a cewarsa ke zaman babban alhaki na gwamnatin kasar.

“Yadda duk aka yi sulhu ne fada ne a kwato su, kuma maganar tsoma bakin mutanen kasashen waje mun dauka hanya ne na kwato yaran nan amma babu wani mai hankali da tunanin da zai jawo kasashen waje cikin harkarsa ta cikin gida, amma a yanayin da muka samu kanmu bamu da zabi, duk yadda zamu yi mu kwato su sai muyi”

Rikicin da ya share shekaru hudu ya kai ga asarar dubbai na rayuka dai ya kai ga sauya salo a idanun mahukuntan kasar da a makon jiya shugaban ta Goodluck Jonathan ya ce yana da buri na ganin bayan gwamnatinsa ne.

'Yan matan sun Kai makonni shidda yanzuHoto: picture alliance/abaca

Kalaman kuma da daga dukkan alamu suka kama hanyar nunin yatsa ga shugabannin yankin da suka share lokaci suna adawa bisa manufofin gwamnatin kasar a siyasance da ma bayan nan.

To sai dai kuma a cewar Adamu Chiroman basu ta cewa a tunanin shugaban kasar da ke kara nuna alamun rudewa a cikin rikicin

“Sai ku tambayi shugaban kasar, shi ya kamata ku tamabaya”

Abun jira a gani na zaman mafitar rikicin da daga dukkan alamu ke kara barazana ga makomar kasar dama zabukan tarrayar da kasar ke shirin fuskanta a badi.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Pinado Abdu Waba