Viele Tote beim Selbstmordanschlag im Jemen
May 22, 2012Ƙasar Yemen, wadda ke gudanar da shagulgulan cika shekarui 22 da sake haɗewar ta a wannan Talatar, ta fuskanci harin ƙunar baƙin wake daya janyo mutuwar kimanin sojojin ta 96 a dai dai lokacin da suke gudanar da fareti a Sana'a babban birnin ƙasar. Sai dai kuma hakan bai hana shugaban Yemen Abd Rabu Mansour Hadi halartar wani faretin da suka yi a safiyar wannan Talatar ba a matsayin wani ɓangare na bukin sake zagowar ranar amma kuma da wani baƙin ƙyalle a gefen sa, wanda ke matsayin alamar nuna juyayi.
A jawabin daya yiwa al'ummar ƙasar, shugaba Hadi yayi alƙawarin daƙile ƙungiyar alQaidah, wadda ta ɗauki alhakin ƙaddamar da harin na wannan Litinin kamar yanda shima babban hafsan tsaron ƙasar Yehya Mohammed Saleh ya jaddada tunda farko:
" Ya ce muna bada tabbacin cewar mu - a rundunar tsaro da kuma na sojin Yemen za mu mayar da martanin daya dace ga duk wani ƙalubale kuma za mu tinƙari waɗannan ɓata-gari, har sai mun shafe su tare da tsarkaka Yemen daga irin munanan abubuwan dake tattare da ita."
Jamus ta bi sahu wajen yin sukar harin Yemen
Tuni ƙasashen duniya daban daban da suka haɗa da Amirka da Birtaniya da kuma Jamus suka bi sahun yin tofin Allah tsine da harin, wanda minisan kula da harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya ce ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen bayar da gudummowar kawo ƙarshen sa:
"Ina sukar wannan harin ta'addanci na Yemen da babbar murya. Ba za mu yarda ayyukan ta'addanci su yaɗu a duniya ba. za mu ci gaba da bayar da goyon bayan yunƙurin mayar da ƙasar kan tafarkin dimoƙraɗiyya da kuma aikin gwamnatin Hadi. Mutanen da ke adawa da shirin sasanta rikicin Yemen ne suke neman mayar da hannun agogo baya ta hanyar tayar da bama-bamai. Mu da sauran ƙasashen duniya muna yin tir da wannan mataki na su.
Muna miƙa jajenmu ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu. Abin da muka sa a gaba a siyasance shi ne neman haɗin kan ƙasar Yemen ciki har da baiwa shugaba Hadi goyon bayan da ya ke buƙata."
Shi ma manzo na musamman da Majalisar Ɗinkin Duniya ta tura zuwa ƙasar ta Yemen Jamal Ben Omar bayyana harin ƙunar baƙin waken yayi da cewar alamar ƙaruwar mayaƙan ƙungiyar alQa'ida ne a yankin, yana mai cewar tilas ne al'ummomin ƙasa da ƙasa su tashi tsaye wajen kawo ƙarshen ta :
" Ya ce abinda ya fito fili a yanzu shi ne cewar alQa'ida ce ke da iko da yankin kudancin Yemen, kuma mai yiwuwa adadin su na ƙaruwa ne ya zuwa ɗaruruwa ko ma dubbanni. A 'yan makonnin da suka gabata sun ƙaddamar da farmaki akan barikokin soji daban daban daya rutsa da mutane da dama, kuma sun cafke wasu sojojin."
A martanin da ƙungiyar alQa'ida reshen ƙasashen larabawa, wadda ta ɗauki alhakin ƙaddamar da harin ƙunar baƙin waken ta yi, cewa ta yi manufar sa shi ne kissar ministan kula da harkokin tsaron Yemen da kuma sauran shugabannin dake taka rawa a hare haren da Amirka ke jagorantar ƙaddamarwa a lardin Abyan dake kudancin ƙasar, wanda tun cikin watan Mayun bara ne ke ƙarƙashin ikon mayaƙan ƙungiyar.
Alƙaluma dai na nuni da cewar mutane 234 suka mutu a hare haren na Abyan, waɗanda suka haɗa da mayaƙan alQ'aida 158 da sojoji 41 da mayaƙan sa kai 18 game da fararen hula 17.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe