1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

131111 Syrien Proteste

November 14, 2011

A yayin da hukumomin Siriya ke ci gaba da yin fito-na-fito tare da masu boren nuna adawa, Rasha ta yi suka ga matakin da ƙungiyar Larabawa ta ɗauka na dakatar da wakilcin Siriya

Zauren taron ƙungiyar Larabawa a birnin alqahiraHoto: dapd

Ƙasashe da kuma sassa daban daban a duniya sun fara tofa albarkacin bakin su game da matakin da ƙungiyar ƙasashen Larabawa ta ɗauka na korar ƙasar Siriya daga cikin ta, bisa abina ta ce gazawar hukumomin Siriya su aiwatar da shawarwarin da ƙungiyar ta gabatar mata domin kawo ƙarshen rigingimun dake faruwa a ƙasar cikin watanni baya bayan nan.

A martanin da ƙasar Rasha ta mayar dangane da matakin, ta zargi ƙasashen yammacin duniya musamman Faransa da Amirka da laifin munafunci, inda wasu ƙasashen kuma ke samar da makamai ga 'yan adawar Siriya a fito na fiton da suke yi tare da hukumomin ƙasar, abinda ministan kula da harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya ce abin taƙaici ne cewar babu wanda ke faɗin komi akan makaman da ake yin fasakwaurin su ƙasar Siriya ta hanyar ƙasashen Iraƙi da kuma Turkiyya, yana mai zargin matakin da ƙungiyar ƙasashen Larabawa ta ɗauka da cewar bai dace ba, kuma yin watsi da wata kyakkyawar damar kawo ƙarshen tashe-tashen hankulan ne.

Hoto: AP

'Yan adawar Siriya suka ce ba gudu, ba ja-da baya

Sai dai a nasu ɓangaren, 'yan adawar ƙasar ta Siriya sun bayyana farin cikin su ne ga matakin, wanda ɗaya daga cikin jiga-jigan adawa a ƙasar Louay Hussein, ya ce ƙungiyar ba ta da wani zaɓin daya wuce hakan, dubi da watsi da hukumomin Siriya suka yi da abubuwan da ta zayyana:

" Ya ce a fili yake cewar, wannan matakin zai sauya lamura. Babban abinda ƙungiyar Larabawa ke son ganin ya wanzu ta hanyar ɗaukar wannan matakin shi ne buɗe ƙofa ga al'ummomin ƙasa da ƙasa da kuma kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya su tsoma bakin su cikin rigingimun dake faruwa a ƙasar Siriya."

Su kuwa magoya bayan shugaba Bashar al-Assad na Siriya Allah wadai ne suka yi da matakin tare da gudanar da jerin gwanon yin suka ga ƙasashen da suka jefa ƙuri'ar amincewa da ƙudirin sallamar ƙasar:

Jerin gwanon magoya bayan gwamnatin dai ya kai ga jefa duwatsu da gilasai akan ofisoshin jakadancin Saudiyya da na Qatar bisa rawar da suka taka wajen ɗaukar matakin, kana da na jakadancin Turkiyya da kuma Faransa a Damascus, bisa kiraye-kirayen da suka daɗe suna yi na neman tilastawa gwamnatin Siriya ta amince da biyan buƙatun masu zanga-zangar adawa da gwamnatin, waɗanda kuma ke cewar sannu a hankali, sai sun cimma gaci:

"Wannan mutumin cewa yake duk da cewar shawarar da ƙungiyar Larabawa ta zartar ta zo a maƙare, amma sannu a hankali muna ƙara samun ƙarfi a idanu duniya, kuma da yardan Allah ko ba jima- ko ba daɗe sai mun yi nasara. "

Wannan matar kuwa tana cewa ne mu 'yan Siriya mun daɗe muna jiran samun tabbaci daga ƙungiyar ƙasashen Larabawa na yin Allah wadai da Bashar da kuma ɗaukacin muƙarraban sa."


Walid al- Moallem, ministan kula da harkokin wajen SiriyaHoto: picture-alliance/landov

Siriya ta bayyana ƙudirin kare ofisoshin jakadancin ƙetare

Sai dai a yayin da ake ci gaba da yin taƙaddama a tsakanin masu adawa da kuma farin ciki ga matakin da ƙunggiyar Larabawar ta ɗauka, a ƙarshen mako kuma take shirin sake wata zama a Larabar nan dake tafe akan batun na Siriya, hukumomin Siriya-ta bakin ministan kula da harkokin wajen ƙasar Walid al-Mouallem afuwa ta nema bisa hare-haren da magoya bayan gwamnati suka ƙaddamar akan ofisoshin jakadancin wasu ƙasashe a birnin Damascus tare da yin alƙwarin cewar ƙasar za ta sauke nauyin daya rataya a wuyanta na bada kariya ga ofisoshin da kuma ɗaukar matakin hana sake afkuwar hakan.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou