1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jinkirta zaben gwamnoni ya haifar da muhawara

March 9, 2023

A Najeriya ana ci gaba da mayar da martani bayan hukumar zaben kasar ta jinkirta lokacin zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohin kasar.

Najeriya | Zabe | Mahmood Yakubu
Farfesa Mahmood Yakubu shugaban hukumar zaben NajeriyaHoto: Kola Sulaimon/AFP/Getty Images

Jinkirta zaben gwamnoni da na 'yan majlisun jihohin najeriya, masu ruwa da tsaki da kokari na girka demokaradiyya a cikin  kasar na ci gaba da mayar da martani bisa matakin da ke zaman na ba zata.

Karin Bayani: An dage zaben gwamnoni a Najeriya

Alamun rudani a cikin zaben gwamnonin dai ya faro ne bayan da kotun zabe na shugaban kasar ta ce ta bai wa manyan jam'iyyun adawa na kasar guda biyu damar kallon kayan zaben.

Jaridun NajeriyaHoto: Emmanuel Osodi/AA/picture alliance

Abin da kuma da ya tayaf da hankalin hukumar zaben da ta ce tana bukatar kari na lokaci da nufin sauyin fasalin na'urar BVAS mai tantance masu zaben.

Wani hukuncin kotun da yazo kasa da hawoyi 72 da fara yin zaben dai ya gaza sauya tunani na hukumar da ke neman kaucewa sake tafka kuskuren da ya mamaye sahihancin zaben shugaban kasar.

Buba Galadima dai na zaman jigo a cikin jam'iyyar NNPP da kuma ya ce hukumar zaben INEC tai nisa a cikin rudani. Yain da Auwal Musa Rafsanjani shugaban kungiyar 'yan kallon cikin gida ta TMG ya ce suna shirin dibga asara sakamakon mataki na hukumar INEC, ganin tilas 'yan kallo na ciki da wajen kasar su kara yawan kudin da suke kashewa saboda sauya lokacin.